Ana Jiran Hukuncin Kotun Koli, INEC Ta Shirya Zaɓukan Cike Gurbi a Kananan Hukumomi 6 Na Kano

Ana Jiran Hukuncin Kotun Koli, INEC Ta Shirya Zaɓukan Cike Gurbi a Kananan Hukumomi 6 Na Kano

  • INEC ta bayyana cewa ta kammala dukkan wasu shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbi na yan majalisar dokokin jihar Kano guda 3
  • Kwamishinan zaben jihar, Abdu Zango, ya ce jami'ai sun shirya tsaf domin gudanar da sahihin zaɓe a watan Fabrairu
  • Ya yabawa rundunar yan sanda bisa ware jami'an da zasu yi aikin tabbatar da tsaro a ranar zaɓen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa ta kammala duk wasu shirye-shiryen gudanar da zaɓukan cike gurbi na ƴan majalisar dokokin jihar.

Zaben cike gurbin mambobin majalisar da INEC zata yi a Kano sun kunshi mazaɓun Kunchi/Tsanyawa, Kura/Garin Malam da Rimin Gado/Tofa.

Kara karanta wannan

Yan sanda, sojoji da wasu hukumomin tsaro 5 sun karɓi kyautar motocin aiki sama da 100 daga gwamna

Shugaban hukumar zabe ta ƙasa INEC, Mahmud Yakubu.
REC: INEC Ta Kamma Shirin Gudanar da Zabukan Cike Gurbi a Jihar Kano Hoto: INECNigeria
Asali: Getty Images

Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, INEC ta tsara gudanar da zaɓukan cike gurbi ne ranar 3 ga watan Fabrairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan zaɓe REC na jihar Kano, Abdu Zango, ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a ofishin INEC na Kano ranar Talata.

A kalamansa ya ce:

"Mun shirya gudanar da zaben cike gurbi, jami'an da muka bai wa horo sun shirya tsaf domin gudanar da sahihi kuma karɓabben zaben maye gurbi a kananan hukumomi shida.
"Zamu gudanar da zabe a mazabu 66 da ke fadin kananan hukumomi shida na jihar Kano waɗanda abun ya shafa kuma duk wanda bai da katin zaɓe ba zai samu damar jefa kuri'a ba."

INEC ta fara rabon kayayyakin zaɓe

Ya ce tuni hukumar INEC ta aike da kayan zabe masu muhimmanci da sauran su ga dukkanin kananan hukumomin da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin gwamnonin jihohi 4 da za su san makomarsu a Kotun Koli a makon nan

Zango ya ƙara da bayanin cewa za a yi amfani da na'urar BIVAS a yayin zaben cike gurbin da nufin tabbatar da an yi sahihin zabe kuma ingantacce.

Kwamishinan zaben Kano ya yabawa rundunar ƴan sanda bisa ware dakarun da zasu samar da isasshen tsaro yayin wannan zaben cike gurbi da ke tafe.

Bola Tinubu ya gayyaci ministan cikin gida

A wani rahoton kuma Tinubu ya kirawo ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, zuwa fadar shugaban ƙasa ranar Talata, 9 ga watan Janairu, 2024.

Shugaban ƙasar ya bada wannan umarnin kiran ne biyo bayan zargin cewa Betta Edu ta bada wata kwangila ga kamfani mai alaƙa da Tunji Ojo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262