Shugaba Tinubu Ya Kori Wasu Manyan Mutane 2 Da Buhari Ya Naɗa, Ya Faɗi Muhimmin Dalili

Shugaba Tinubu Ya Kori Wasu Manyan Mutane 2 Da Buhari Ya Naɗa, Ya Faɗi Muhimmin Dalili

  • Bola Ahmed Tinubu ya kori wasu shugabannin hukumomi biyu waɗanɗa Muhammadu Buhari ya naɗa a lokacin mulkinsa
  • Shugaban ƙasar ya basu umarnin miƙa ragamar jagoranci ga babban ma'aikacin da ke ƙasa da su nan take
  • Matakin na zuwa ne awanni kalilan bayan Tinubu ya dakatar da Betta Edu, ministar harkokin jin kai da yaƙar talauci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tsige wasu manyan hadiman gwamnatin tarayya waɗanda magabacinsa, Muhammadu Buhari ya naɗa.

A rahoton TVC, waɗanda Tinubu ya kora daga aiki sun haɗa da shugaban hukumar FCCPC (Federal Competition and Consumer Protection Commission), Babatunde Irukera.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Kori Wasu Mutum Biyu da Buhari Ya Nada, Ya Bayyana Dalili Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Bayan shi kuma shugaban ƙasan ya tsige darakta janar kuma shugaban hukumar BPE (Bureau of Public Enterprises), Alexander Ayoola Okoh.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin masu mukamin da Tinubu ya nada kuma ya dakatar/cire su kasa da shekara 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki na tsige shugabannin hukumomin biyu na tarayya na kunshe ne a wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban ƙasa, ranar Litinin, 8 ga watan Janairu.

Bayo Onanuga, babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru ya wallafa sanarwan a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Tinubu ya kore su daga aiki nan take

Sanarwan ta umarci waɗanda matakin ya shafa su miƙa harkokin mulki ga babban ma'aikacin da ke ƙasa da su a hukumomin yayin da korarsu ta fara aiki nan take.

Manyan ma'aikatan da zasu miƙa wa ragamar hukumomin za su ci gaba da kula da harkokin waɗannan hukumomin har zuwa lokacin da shugaban ƙasa ya naɗa sabbi.

Sanarwan mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ta ce:

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

"Ana umurtan korarrun shugabannin hukumomi su miƙa ragama ga manyan jami'an gwamnati da ke ƙasa da su a wurin gabanin naɗa waɗanda zasu maye gurbinsu."

Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan shugaba Tinubu ya dakatar da ministar harkokin jin ƙai da walwala, Dokta Betta Edu.

Gwamnonin da kotum ƙoli ta shirya yanke hukunci

A wnai rahoton Ana sa ran kotun kolin Najeriya za ta raba gardama kan sahihancin nasarar gwamnoni 21 a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Mun tattara muku manyan shari'o'in zaben gwamnan da zasu fi ɗaukar hankali a makon da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262