APC Ta Bayyana Wanda Zai Gaji Ministan Tinubu Bayan Ya Yi Murabus Daga Kujerarsa
- A yau Asabar 6 ga watan Janairu aka gudanar da zaben fidda gwani a neman tsakarar kujerar mazabar Ebonyi ta kudu
- Farfesa Anthony Okorie ya samu damar lashe zaben da kuri’u 281 daga cikin 285 da aka kada a zaben a jihar Ebonyi
- An gudanar da zaben fidda gwanin ne don maye gurbin Sanata Dave Umahi wanda ya karbi mukamin Minista a gwamnatin Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ebonyi – Anthony Okorie ya samu damar mallakar tikitin jam’iyyar APC a zaben sanatan Ebonyi ta Kudu da za a gabatar.
Okorie ya samu kuri’u 281 daga cikin 285 da aka kada yayin zaben fidda gwani da aka yi a yau Asabar 6 ga watan Janairu.
Yaushe aka gudanar da zaben fidda gwanin?
The Nation ta tattaro cewa Okorie shi ne dan takara daya tilo daya fito neman takarar kujerar da za gudanar da zabe a watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da zaben fidda gwanin ne don maye gurbin Sanata Dave Umahi wanda ya karbi mukamin Minista a gwamnatin Tinubu.
Okorie wanda Farfesa ne a Jami’ar Tarayya ta Kimiyya a Owerri da ke jihar Imo ya yi alkawarin cire wa jama’ar yankin kitse a wuta, cewar Daily Trust.
Yaushe za a gudanar da zaben cike gurbi?
Wannan na zuwa ne bayan kanin tsohon gwamnan jihar, Austin Umahi ya janye daga takarar neman kujerar yayansa, Dave Umahi.
Umahi dai ya ajiye kujerar sanatan ne bayan Shugaba Tinubu ya nada shi mukamin Ministan Ayyuka a gwamnatinsa.
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanya 3 ga watan Faburairu a matsayin ranar gudanar da zaben cike gurbi.
Kanin Ministan Tinubu na neman takarar kujerarshi
A wani labarin, Austin Umahi, kani a wurin tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya nuna sha'awar tsayawa takara.
Austin ya nuna sha'awar gadar kujerar yayansa da ya bari ta Sanatan mazabar Ebonyi ta Kudu a karkashin jam'iyyar APC.
Daga bisani ya janye kudirin nasa bayan an tura kujerar zuwa wani yanki daban wanda ba na shi ba.
Asali: Legit.ng