Shugaba Tinubu Ya Bai Wa Sanatoci Buhunan Shinkafa Su Rabawa Talakawa? Gaskiya Ta Bayyana

Shugaba Tinubu Ya Bai Wa Sanatoci Buhunan Shinkafa Su Rabawa Talakawa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Majalisar dattawan ta musanta rahoton cewa sanatoci sun karbe tallafin kayan abinci na N200m kowanensu daga Tinubu domin rabawa talakawa
  • Shugaban kwamitin watsa labarai, Adeyemi Adaramodu, ya karyata jita-jitar wacce ta fito daga bakin hadimin shugaban ƙasa
  • Mai taimakawa shugaba Tinubu kan harkokon sadarwa na zamani ya tabbatar da cewa an fara rabawa sanatoci da yan majalisar wakilai kayan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta karyata rahoton da ya yi ikirarin cewa sanatoci sin karɓe tallafin buhunan shinkafa na kimanin N200m daga shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Majalisar ta musanta rahotan da kafafen yada labarai suka yada cewa Sanatoci sun karbi shinkafar Naira miliyan 200 daga Tinubu domin rabawa al’ummar mazabunsu a matsayin tallafin kirsimeti.

Kara karanta wannan

Ku raba mana shinkafar Tinubu yanzu, Kungiyar kare hakkin musulmi ta fadawa yan majalisa

Majalisar dattawa ta karyata rahoton kafafen watsa labarai.
Shugaba Tinubu Ya Bai Wa Sanatoci Buhunan Shinkafa Su Rabawa Talakawa? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: SanateNGR
Asali: Twitter

Shugaban kwamitin midiya da yaɗa labarai na majalisar dattawa, Sanata Adeyemi Adaramodu, ne ya yi wannan karin haske ranar Jumu'a, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wata majiya a majalisar dattawan ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce har yanzu wasu daga cikin kayayyakin tallafin shinkafa ba su isa ga sanatoci ba.

Daga ina maganar rabon kayan tallafin ta taso?

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin sadarwa na zamani, Olusegun Dada, ranar Alhamis ya tabbatar da rabon kayayyakin agaji na Naira miliyan 200 ga sanatoci.

Ya kuma kara da cewa an raba wannan tallafi na kayayyaki da suka kai na Naira miliyan 100 ga mambobin majalisar wakilai.

Ya ce:

"Bayan jinkirin da aka samu, a yanzu zan iya tabbatar da cewa Sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai sun fara karɓan kayan tallafin da Gwamnatin Tarayya ta ware wa al’ummar mazabunsu domin rage raɗaɗi."

Kara karanta wannan

Sojojin Sama Sun Kashe Shugaban Yan Ta'adda, Ba'a Shuwa, da Wasu Mayakansa a Borno

"Kowane mamban majalisar wakilai zai karɓi kayan tallafin da suka kai na N100m yayin da kowace mazaɓar sanata za a raba kayan rage radadi na N200m"

Majalisar dattawa ta musanta

Da yake maida martani kan wannan ikirarin, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce har yanzu bai samu wani kayan agaji daga gwamnatin tarayya ba, Premium Times ta ruwaito.

Adaramodu ya ce ya raba kayan abinci da kudi ga al’ummar mazabarsa domin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara amma da kuɗinsa ya siyo kayan ba na FG bane.

Abba ya ƙara samun goyon baya a Kano

A wani rahoton kun ji cewa Yayin da kotun koli ke shirye-shiryen yanke hukunci, Gwamna Abba ya samu ƙarin goyon bayan jama'a a jihar Kano

Dubannin mambobin NNPP galibi mata a karamar hukumar Dawakin Tofa sun gudanar da addu'ar Allah ya ba Abba nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262