Ana Daf da Yanke Hukunci, Gwamnan Arewa Ya Tura Sako Ga Kotun Koli Kan Tsiyar da Aka Tafka Masa
- Yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli, Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya tura sako
- Gwamnan ya bayyana cewa ba a yi masa adalci ba yayin hukuncin Kotun Daukaka Kara a zaben jihar
- Caleb ya ce kawai yanke hukunci aka yi inda ya ce ya ba da hujjoji guda takwas ga kotun amma daya kawai aka yi amfani da shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar plateau – Gwamna Caleb Mutfwang na jihar plateau ya nuna damuwa kan rashin adalci da aka yi masa a shari’ar zaben jihar.
Gwamnan ya ce kwata-kwata ba a ba shi damar yin bayani ba daga bangarenshi yayin hukuncin Kotun Daukaka Kara.
Mene Gwamna Caleb ke cewa kan shari'ar zaben?
Caleb ya ce kawai yanke hukunci aka yi inda ya ce ya ba da hujjoji guda takwas ga kotun amma daya kacal aka yi amfani da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce fatali da hujjoji bakwai daga cikin takwas ya saba ka’idar Kotun Koli inda ya ce ya kamata a zayyano hujjojin a gabanta.
Ya kuma roki Kotun Koli da ta ayyana shi a matsayin zababben gwamnan jihar ba tare da bata lokaci ba, cewar TheCable.
Mutfwang ya bayyana haka ta bakin babban lauyansa, Kanu Agabi inda ya ce doka ta bayyana cewa duk lokacin da aka samu kuskure dole a gyara ta.
Wace bukata Caleb ya tura ga Kotun Koli?
Ya ce:
“Hujjoji masu girma guda takwas aka gabatar a gaban kotun, amma abin takaici guda daya kacal aka yi amfani da shi tare da watsar da guda bakwai.
“Kotun ta bayyana cewa karamar kotun dole ta gabatar da dukkan hujjojin da ke gabanta, bai kamata a takaita zuwa hujja daya ba.
“Hakan shi zai bai wa Babbar Kotun damar sanin dukkan korafe-korafen watakila ta yi duba ga wasu hujjoji da karamar kotun ta yi fatali da su.”
Gwamna Caleb ya kara tabbatar da cewa tun ba a ba shi damar yin bahasi ba, Kotun Koli ya kamata ta tabbatar da shi a matsayin gwamna.
Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli a jihohin Kano da Plateau da kuma Nasarawa, cewar Leadership.
A Kano, Kotun Daukaka Kara ta sake rusa zaben Gwamna Abba Kabir na jam’iyyar NNPP saboda wasu kura-kurai yayin tsayawa takarar gwamna.
Abba Kabir ya fara biyan kudin diyyar rusau
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya fara biyan biyan kudaden diyyar rusau.
Gwamnan ya amince da fara biyan naira biliyan daya daga cikin biliyan uku da ya amince da su a kwanakin baya.
Asali: Legit.ng