Ciyamomin Kananan Hukumomin da Ke Takun Saka da Gwamna Sun Sake Daukaka Kara, Sun Fadi Dalilai

Ciyamomin Kananan Hukumomin da Ke Takun Saka da Gwamna Sun Sake Daukaka Kara, Sun Fadi Dalilai

  • An ci gaba da kai ruwa rana bayan dakatattun ciyamomin kananan hukumomi 18 da kansiloli 33 sun daukaka kara a jihar
  • Ciyamomin guda 18 da kansiloli 33 sun shigar da karar ce don kalubalantar karamar kotu da kuma matakin gwamnan
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar ya dakatar da ciyamomin da kansiloli a jiya Laraba 3 ga watan Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo – Ciyamomin kananan hukumomin da aka dakatar a jihar Ondo sun daukaka kara zuwa kotu.

Ciyamomin guda 18 da kansiloli 33 sun shigar da karar ce don kalubalantar karamar kotu a ranar 1 ga watan Disamba, Tribune ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rantsar da sabbin ciyamomi 38 da mataimakansu, sun kama aiki gadan-gadan

Ciyamomin kananan hukumomi sun daukaka kara kan dakatar da su
Gwamna Lucky ya dakatar da su ne a jiya Laraba. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Yaushe gwamna ya dakatar da ciyamomin a Ondo?

Idan ba a mantaba, Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar ya dakatar da ciyamomin da kansiloli a jiya Laraba 3 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ciyamomin, Banji Ayelakin ya rubuta takarda ta hannun sakataren din-din-din daga ma’aikatar kananan hukumomin kan karar da suka shigar.

Takardar ta ce:

“Mu ne lauyoyin ciyamomin kananan hukumomi da kansiloli a jihar Ondo wanda shi ne dalilin rubbuta wannan takarda.”

Wane mataki Gwamna Lucky ya dauka kan ciyamomin?

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu a ranar 27 ga watan Disamba a kasar Jamus, cewar Channels TV..

A kwanakin baya, Babbar Kotun jihar ondo da ke zamanta a Akure ta dakatar da rantsar da ciyamomin guda 18 da kansilolin 33.

Hakan shi ya sanya gwamnatin jihar ta umarci dukkansu su bar ofisoshinsu har zuwa lokacin yanke hukuncin kotun da PDP ta shigar, kamar yadda Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Tarayya ta bai wa Abba Kabir wa'adin mako 1 kan karar da aka shigar da shi

Gwamna Lucky ya dakatar da ciyamomin 18 a Ondo

A wani labarin, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya dakatar da dukkan ciyamomin kananan hukumomin jihar 18 da kuma kansiloli 33 a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan babbar kotun jihar ta dakatar da rantsar da ciyamomin da kuma kansiloli a jihar.

Hakan ya biyo matakin farko da gwamnan ya dauka bayan rasuwar mai gidansa, Rotimi Akeredolu a kasar Jamus bayan fama da jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.