Abba Kabir Yusuf Ya Nada Fasto da Ibo a Matsayin Masu Ba Gwamna Shawara a Kano
- Abba Kabir Yusuf ya nada karin masu ba shi shawara da za su taimakawa gwamnatinsa a Kano
- Mai girma gwamnan ya rantsar da wani Fasto mai suna Andrew Ma’aji a cikin hadimansa a gwamnati
- Chukwuma Innocent Ogbu yana cikin sababbin masu ba gwamnan Kano, Abba Gida Gida shawara yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Mai girma Abba Kabir Yusuf ya cigaba da nade-naden mukamai a matsayin gwamnan jihar Kano.
Kamar yadda sanarwa ta gabata, gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sakatarori da karin hadimai a Kano.
Abba ya nada mukamai a Kano
An rantsar da manyan sakatarorin gwamnati 21 da kuma masu bada shawara na musamman 15 ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce ya zabi wadannan mutane ya ba su mukami ne saboda cancanta, nagarta da lura da tarihinsu.
Daily Nigerian ta rahoto Abba Kabir Yusuf yana jan kunnen wadanda aka ba mukami da cewa ka da su ci amana.
Gwamnan Kano ya yi rigima da SSG?
A wajen taron aka ji labari cewa gwamnan ya yi magana game da rade-radin rigimarsa da Dr. Abdullahi Baffa Bichi.
Gwamnan da aka fi sani da Abba Gida Gida ya shaidawa duniya bai yi fada da sakataren gwamnatin na Kano ba.
Kano: Fasto da Ibo sun samu kujera
Abdullahi Ibrahim, mai taimakawa gwamnan a kafofin sadarwa na zamani ya yi karin haske a kan nadin mukamai.
Hadimin gwamnan ya yi magana a dandalin X, ya ce daga cikin wadanda aka rantsar akwai Fasto Andrew Ma’aji.
Haka zalika Cif Chukwuma Innocent Ogbu ya samu shiga a matsayin mai bada shawara a ofishin gwamnan na Kano.
Gwamnatin Kano tana tafiya da kowa
Abba Yusuf ya yi hakan ne ba domin komai ba sai ganin ya jawo kowa a gwamnatinsa da nufin samun hadin-kai.
Ba wannan ne karon farko da aka yi irin wannan a Kano mai miliyoyin jama'a ba, ana sa ran nadin zai kawo zaman lafiya.
Bebeji ta yi sabon shugaba
A rahoton da aka fitar a baya, ana da labarin an nada Aliyu Ibrahim Kuki a matsayin shugaban karamar hukumar Bebeji.
Alhaji Aliyu Ibrahim Kuki ne ya canji tsohon shugaban karamar hukumar da ya rasu a 2023 watau Marigayi Sani Kanti.
Asali: Legit.ng