APC Na Murna Bayan PDP Ta Sake Shiga Matsala Yayin da Ta Dakatar da Shugabanta Kan Dalili 1 Tak
- Jam’iyyar PDP a jihar Ondo ta dakatar da shugabanta a jihar, Fatai Adams kan wasu zarge-zarge a kansa
- Jam’iyyar ta dakatar da Fatai Adams ne bayan ta zarge shi da yi wa jam’iyyar zagon kasa
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar a wannan shekara da muke ciki ta 2024
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo – Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar ondo, jam’iyyar PDP ta dakatar da shugabanta a jihar.
Jam’iyyar ta dakatar da Fatai Adams ne bayan ta zarge shi da yi wa jam’iyyar zagon kasa, cewar Channels TV.
Mene dalilin PDP na dakatar da shi?
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar a wannan shekara da muke ciki ta 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a yau Talata 2 ga watan Janairu ta ce Kwamitin gudanarwa ta jam’iyyar ta dakatar da Fatai kan wasu zarge-zarge.
Jam’iyyar har ila yau, na zargin Fatai wanda aka zaba a watan Agustan 2020 da zargin jawo wa jam’iyyar zubewar mutuncinta.
Daily Trust ta tattaro cewa mambobin kwamitin tara ne suka sanya hannu a takardar korar Fatai.
Wannan mmataki da suka dauka ya yi dai-dai da sashi na 58 na kundin tsarin jam’iyyar wanda aka yi wa gyaran fuska.
Mene PDP ke cewa kan Fatai?
Sanarwar ta ce:
“Bisa sashi na 58 na kundin tsarin mulkin PDP da aka yi wa gyaran fuska a 2017, kwamitin ta dakatar da Mista Fatai Adams a matsayin shugabanta.
“An dakatar da Adams ne kan zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa inda ya ke neman bata wa PDP suna.
“An kuma shawarce shi da ya gurfana a gaban kwamitin ladabtarwar jam’iyyar don gudanar da bincike nan da mako daya.”
Sanarwar ta kara da cewa jam’iyyar ta yi gargadin cewa za ta dauki mummunan mataki kan shiga lamuran jam’iyyar daga APC mai mulkin jihar.
Har ila yau, Adams ya yi fatali da korar ta shi da mambobin kwamitin suka yi ba bisa ka’ida ba.
Ya ce wannan dakatar da shi da aka yi kawai bita da kullin siyasa ce don biyan bukatar kansu kan zaben Majalisar Tarayya da za a yi.
APC ta magantu kan shari’ar Kano
A wani labarin, Jam’iyyar APC ta bayyana kwarin gwiwarta kan shari’ar zaben gwamnan Kano.
Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukncin Kotun Koli bayan ta tanadi hukunci kan shari’ar.
Asali: Legit.ng