Abba Ko Gawuna? An Hango Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Koli Duba da Wasu Dalilaia

Abba Ko Gawuna? An Hango Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Koli Duba da Wasu Dalilaia

  • Wasu ‘yan APC sun bayyana kadan daga abin da zai iya faruwa a hukuncin da za a yanke a kotun koli tsakanin Abba da Gawuna
  • Sun hango cewa, akwai hasken Gawuna ya yi nasara a hukuncin da za a yanke, shugaba ya bayyana dalili
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana da jiran tsammani kan wanda za a bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben Kano

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Kano - Kungiyar tsofaffin mashawarta a a APC ta ce akwai 99.9% cikin 100% na kyautata zaton samun nasara a hukuncin kotun koli da ake jira a kan rikicin zaben gwamnan Kano.

Shugaban kungiyar Dakta Abbati Bako ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: An yi zanga-zanga a Kano kan takaddamar zaben gwamna

Yayin da yake taya dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa Murtala Sule Garo murnar nasara, ya ce ko shakka babu hukuncin da aka yanke a baya zai samu a kotun koli.

Gawuna ne zai yi nasara ba Abba ba, inji 'yan APC
Gawuna zai yi nasara a kotu ba Abba ba, inji 'yan APC | Hoto: Abba Kabir Yusuf, Nasiru Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman Abbati Bako kan nasarar Gawuna

A cewarsa:

“Ina son amfani da wannan dama wajen taya zababben gwamnanmu Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa Murtala Sule Garo murna a zaben da ya gabata kamar yadda kotun sauraren kararrakin zabe da kotun daukaka kara suka bayyana.”

Ya kuma bayyana cewa, da yawan mutanen jihar Kano na Allah-Allah Gawuna ya samu nasara a kotun kotun.

Abin da gwamnatin APC za ta kawo a Kano

A cewarsa, suna tsammanin samun mulki na gari daga dan takarar na jam’iyyar APC mai mulkin kasa a yanzu.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana game da shari’ar Kano, inda wasu ke ganin ba a yiwa jam’iyyar NNPP adalci ba kwata-kwata, New Telegraph ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shari'ar Zaben Kano: Ina da tabbacin samun nasara, Abba Kabir ya magantu, ya roki Kanawa

Abba dan asalin NNPP ne?

Boniface Aniebonam, wanda ya kafa jam’iyyar NNPP, ya roki dakarun da ke ciki da wajen jam’iyyar da su baiwa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano damar fuskantar mulki cikin kwanciyar hankali.

Aniebonam, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin amintattu na NNPP, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Legas, cewar rahoton Vanguard.

Kalaman nasa na zuwa ne biyo bayan cece-kucen da aka samu kan hukuncin da kotu ta yanke na korar Gwamna Abba da zamansa dan jam’iyyar NNPP a zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.