Yan Najeriya Sun Yi Martani Yayin da Shugaba Tinubu Ya Yi Wani Abin Ban Mamaki a Bidiyo

Yan Najeriya Sun Yi Martani Yayin da Shugaba Tinubu Ya Yi Wani Abin Ban Mamaki a Bidiyo

  • Shugaba Bola Tinubu ya jawo martani daga ƴan Najeriya lokacin da ya dakatar da jami'an tsaronsa hana shi yin musabaha da Rasak Okoya
  • Tinubu wanda ya je Legas domin bikin Kirsimeti, an dauke shi a cikin wani faifan bidiyo da ya yi watsi da matakin dakatar da gaisuwarsa da ɗan kasuwan
  • Wasu ƴan Najeriya da suka yi tsokaci sun yaba wa shugaban kan yadda ya bambanta tsakanin ƙa’idojin tsaro da alaka mai tsawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana a cikin wani faifan bidiyo da ya hana jami’an tsaro kutse a lokacin da suke musabaha da Rasak Okoya, fitaccen ɗan kasuwa a Legas.

A cikin faifan bidiyon, Tinubu ya daɗe yana musabaha da ɗan kasuwar, kuma an ga Okoya ya riƙe hannun shugaban ƙasan da hannayensa biyu.

Kara karanta wannan

Ba a gama jimamin mutuwar mutum 190 ba, yan bindiga sun sake kai mummunan hari a jihar Plateau

Shugaba Tinubu ya ba da mamaki a Legas
Shugaba Tinubu ya dakatar da jami'an tsaro hana shi gaisawa da Okoya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin dakatar da shi, amma nan take shugaban ƙasa ya hana su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan dai ya faru ne a wani taron da aka gudanar a Legas, inda a halin yanzu Shugaba Tinubu ke hutun Kirsimeti.

Ƴan Najeriya sun yi martani

Wasu ƴan Najeriya sun yi martani kan wannan abin da shugaban ƙasan ya yi.

Ga wasu daga ciki a nan ƙasa:

Sadeeq ya yi nuni da cewa, Shugaba Tinubu ya tunatar da jami’an tsaro tsawon lokacin da ya yi tare da hamshaƙin attajirin na Legas.

Ya rubuta:

"BAT yana nuna cewa ka san irin gwagwarmayar da muka sha tare."

Olomitutu ya ce matakin na Tinubu ya ci karo da abin da abokan hamayyarsa na siyasa suka yi hasashe a kansa a lokacin zaɓe.

Ya rubuta:

"Dama yanzu hannun Tinubu yana aiki? Ina tunanin mutanensu Obimumu sun ce ba zai iya ɗaga hannunsa ba. Dama wannan hannun zai iya aiki da sauiri haka kamar yadda ya dakatar da jami'in DSS ɗinnan cikin sauri? Lol, Tinubu ya riƙe hannun kamar mai tsaron gida yana kama fanareti."

Kara karanta wannan

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP ta fadi laifin Tinubu, ta gaya masa muhimmin abu 1 da ya kamata ya yi

Abob ya yi nuni da cewa jami'in tsaron yana gudanar da aikinsa ne kawai.

Ya rubuta:

"Haƙƙinsu ne, ban da haka, musabahar ta dau tsawon lokaci."

Ƴan Legas Sun Yi Wa Ayarin Motocin Tinubu Ihu

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mazauna jihar Legas sun yi wa ayarin motocin Shugaba Tinubu ihu kan cewa akwai yunwa a ƙasa.

Mutanen dai sun yi hakan ne a yayin da ayarin motocin shugaban ƙasan ke wuce zuwa masallaci domin gudanar da Sallar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng