Jam'iyyar NNPP Ta Cimma Yarjejeniya da APC Kan Shari'ar Gwamna Abba da Gawuna? Gaskiya Ta Bayyana
- Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi magana kan yarjejeniyar da ake cewa ta cimmawa da jam'iyyar APC kan shari'ar gwamnan Kano
- Mai binciken kuɗi na jam'iyyar na ƙasa ya bayyana cewa sam babu wata yarjejeniya da suka cimmawa da APC
- Ya bayyana cewa fatansu shi ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi nasara a kotun ƙoli domin cigaba da ayyukan da yake yi a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi watsi da iƙirarin cewa ta cimma yarjejeniya da jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) kan ƙarar da ta shigar a kotun ƙoli.
Babban mai binciken jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson, shi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar The Punch a ranar Asabar, 30 ga watan Disamban 2023.
Ladipo ya bayyana cewa duk da cewa mutum ba zai iya hana mutane yaɗa jita-jita ba, amma maganar ƙarya ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Babu wata yarjejeniya da NNPP' - APC
Ita ma jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta musanta wata yarjejeniya da jam’iyyar NNPP.
Yarjejeniyar da ake zargin, a cewar shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, tatsuniya ce kawai.
Gwamna Abba Yusuf ya ɗaukaka ƙara a kotun ƙoli a matsayin martani ga hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zabe ta jihar ta yanke.
Kotun zaɓen dai ta soke nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
NNPP ta musanta cimma yarjejeniya da APC
Johnson ya bayyana cewa:
"Abin da kuke ji magana ce ta kan titi kuma ba za ku iya hana tattaunawar titi ta faru ba."
"Ban da tabbacin wani babban jami’i a jam’iyyar zai gaya muku hakan zai iya faruwa. Muna ƙoƙarin samun nasara a kotu kuma Abba Kabir Yusuf zai cigaba da gudanar da ayyuka nagari ga al’ummar Kano."
APC Za Ta Lallasa NNPP a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa Dan takarar sanata a mazabar Kano ta Tsakiya, Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya ce ko an sake zabe APC ce za ta yi nasara.
Zaura wanda ya yi takara a jam’iyyar APC a wannan shekara ya bayyana cewa jam’iyyar ce za ta yi nasara idan da za a sake zaɓe yanzu a Kano.
Asali: Legit.ng