"An Kulla Tuggu" Malami Ya Bayyana Gwamnan PDP da Zai Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC Kwanan Nan
- Wani fitaccen malamin addini a jihar Legas, Primate Elijah Ayodele, ya ce Gwamna Siminalayi Fubara na Ribas zai tsallaka zuwa APC
- Legit Hausa ta tattaro Primate Ayodele na cewa wannan shiri na 'sauya sheƙa' wani ɓangare ne na babban kullin kawar da jam'iyyar PDP
- Mai wa'azin ya yi kira ga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa ta hanzarta dinƙe ɓarakar cikin gida domin toshe wannan yunƙuri
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya ce nan ba da daɗewa ba Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas zai fice daga PDP.
A cewar fitaccen malamin addinin kiristan, Gwamna Fubara zai bar jam'iyyar PDP ya koma babbar jam'iyyar adawa a jihar Ribas watau APC.
"Wike ya shiga gaba a Ribas" Ayodele
Malamin ya bayyana cewa wannan dambarwar siyasar da ke wakana tsakanin Gwamna Fubara da ministan Abuja, Nyesom Wike, "duk shiri ne."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayodele ya yi wannan furucin ne kan rikicin siyasar jihar Ribas a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Alhamis.
A kalamansa ya ce:
"A jihar Ribas, na hango Fubara ya koma APC. Gwamna Fubara ba zai iya kassara Wike ba. Wike ya riga ya shiga gaba kuma tuni Fubara ya tsinci kansa a APC. Bisa haka PDP ku daina wahal da kanku kan Fubara."
"Gwamna Fubara ba zai iya taɓuka komai ba, na riga na faɗi wannan, shiyasa wasu mutane suka tsane shi. Fubara ba shi da ƙarfin da zai tunkari yaƙin, kuma zai tsallake zuwa APC."
"Duk wannan abun shiri ne, komai ya ƙare, sun kulle komai. Saboda haka abinda ya kamata a yanzu, PDP ta yi koƙarin haɗa kawunan 'ya'yanta, ku rubuta kalamai na ku aje."
Jerin gwamnonin da suka ba ma'aikata kyautar kirsimeti
A wani rahoton kuma kuna da labarin wasu gwamnoni sun ƙarƙare 2023 da ƙunshin kyauta mai gwabi ta N100,000 ga ma'aikatan jihohinsu.
Wannan kyautar kuɗi na zuwa ne yayin da mutane ke fama da matsin tattalin arziki wanda ya samo asali daga tuge tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng