2024: Kwanaki 2 da Mutuwar Gwamna, Lucky Ya Manta da Shi Ya Ziyarci Tinubu Kan Wani Babban Dalili

2024: Kwanaki 2 da Mutuwar Gwamna, Lucky Ya Manta da Shi Ya Ziyarci Tinubu Kan Wani Babban Dalili

  • Kwanaki biyu da mutuwar Akeredolu, alamu sun nuna sabon gwamnan ya fara shirye-shiryen tsayawa takara
  • Rahotanni sun tabbatar cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ziyarci Shugaba Tinubu a Legas kan zaben 2024 a jihar
  • Sai dai hadiman gwamnan sun musanta hakan inda suka ce Lucky ya je Legas ne don sanar da Tinubu rashin da aka yi a hukumance

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo – Alamu sun nuna an fara shirye-shiryen zaben shekarar 2024 da za a yi a jihar Ondo.

Vanguard ta tabbatar da cewa Gwamna Lucky Auyedatiwa ya ziyarci Shugaba Tinubu a Legas kan maganar zaben.

Sabon gwamnan Ondo ya fara ziyarar neman takara a 2024
Gwamna Lucky ya ziyarci Tinubu kan shirin siyasar 2024. Hoto: Bola Tinubu, Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Mene silar ziyarar ta Lucky ga Tinubu?

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: Jerin hadiman gwamna da suka yi murabus daga muƙamansu bayan mutuwa ta gitta

Har ila yau, an ruwaito cewa gwamnan har ya fara ganawa da wasu masu ruwa da tsaki kan tsayawa takara a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a kasar Jamus.

Mutuwar marigayin ke da wuya aka rantsar da Lucky a matsayin sabon gwamnan jihar yayin da ake shirin zabe a 2024.

Wata majiya ta tabbatar da cewa Aiyedatiwa ya kai wa Tinubu ziyarar ce don bayyana masa aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar.

Mene martanin hadiman gwamnan?

Sai dai hadiman gwamnan sun musanta hakan inda suka ce gwamnan ya je Legas ne musamman don sanar da Tinubu rahin da aka yi a hukumance.

Sun musanta maganar cewa gwamnan ya je Legas ne don tattauna batun siyasar jihar musamman da zabe ke karatowa.

Idan ba a manta ba a jiya Alhamis ce gwamnan ya ziyarci gidan marigayin a Ibadan inda ya musu ta’aziya ta musamman, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

"Akwai sa hannun wasu mutane a mutuwar Akeredolu", Sowore ya yi zargi

Daga bisani gwamnan ya wuce jihar Legas don ganawa da Shugaba Tinubu yayin da ya ke ci gaba da hutun Kirsimeti.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a tabbatar da cikakken bayani kan ganawar tasu ba a Legas.

Aiyedatiwa ya yi sabbin nade-nade

A wani labarin, sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya fara da nada mukamai guda hudu a jihar awanni kadan bayan rantsar da shi.

Lucky ya nada Ebenezer Adeniyan a matsayin sabon sakataren yada labaransa bayan tsohon sakataren ya yi murabus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.