Akeredolu: Fitaccen Malamin Addini Ya Fadi Wanda Zai Zama Gwamnan Ondo a 2024
- Babban fasto Ifetayo Afinjuomo ya bayyana cewa wani mutum daga yankin Ileoluji/Okeigbo shine zai zama gwamna idan aka yi zaben gwamnan jihar Ondo na gaba
- Hasashen Fasto Afinjuomo na zuwa ne adaidai lokacin da Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo ya kwanta dama
- Legit Hausa ta rahoto cewa Akeredolu, babban lauyan Najeriya, ya mutu a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba yana da shekaru 67 a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Ore, jihar Ondo - Babban faston da ke jan ragamar cocin Dominion Faith, Ore, Ondo, Prophet Ifetayo Afinjuomo, ya ce wani dan siyasa daga yankin karamar hukumar Ile Oluji/Okeigbo na jihar, shine zai lashe zaben gwamnan jihar Ondo a 2024.
Bai dade ba da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da ranar zaben gwamna a jihar Ondo.
Malamin addini ya yi hasashe kan zaben Ondo na gaba
An tsara za a yi zaben gwamnan jihar Ondo a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta rahoto cewa wa'adin mulkin tikitin hadin gwiwa na marigayi Rotimi Akeredolu da Lucky Aiyedatiwa zai kare a ranar 23 ga watan Fabrairun 2025.
Sakon da Prophet Afinjuomo ya wallafa a shafinsa na Facebook na cewa:
"Hasashe kan 2024.
"Najeriya: lokaci ya yi da za a bunkasa.
"Zaben jihar Ondo: Na ga wani mutumin Ileoluji/Okeigbo da zai zama gwamna.
"Kasar Japan: Ku yi wa Japan addu'a, na ga an datse tutarta.
"Mutum daya: Wani sabon tafiya zai tashi daga bangaren Almasihu.
"2024 shekarar karuwata ce. Hallelujah!"
Gwamnan ya rasu ne da safiyar Laraba, 27 ga watan Disamba, 2023.
Diyar Akeredolu ta fatattaki yan jarida
A wani labarin, mun ji a baya cewa diyar Marigayi Rotimi Akeredolu, Ololade, ta fatattaki yan jarida da suka je daukar bayanan ziyarar ta'aziyya da manyan masu fada aji suka kai gidan tsohon gwamnan jihar Ondo a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, diyar tsohon gwamnan ta koka cewa gidan Ibadan gidansu ne mai zaman kansa ba gidan gwamnati ba.
Asali: Legit.ng