Karin Bayani: Gwamnatin Ondo Ta Fitar da Sanarwa, Ta Faɗi Abinda Ya Jawo Mutuwar Gwamna Akeredolu

Karin Bayani: Gwamnatin Ondo Ta Fitar da Sanarwa, Ta Faɗi Abinda Ya Jawo Mutuwar Gwamna Akeredolu

  • Daga ƙarshe gwamnatin jihar Ondo ta sanar da rasuwar Gwamna Oluwarotimi Akeredolu a hukumance ranar Laraba
  • Kwamishinar yaɗa labarai ta jihar, Bamidele Ademola-Olateju, ta ce gwamnan ya rasu yayin da yake jinya a ƙasar Jamus
  • Ta bayyana cewa marigayin ya sha fama da ciwon kansa, wanda ya zama ajalinsa bayan tsawon lokaci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Cikin jimami da kaɗuwa, Gwamnatin jihar Ondo ta sanar da rasuwar Gwamna Oluwarotimi Akeredolu (SAN) a hukumance.

Gwamna Akeredolu na jam'iyyar APC ya cika ne da safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, 2023 bayan fama da doguwar jinya.

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
Gwamnatin Ondo Ya Sanar da Rasuwar Gwamna Akeredolu, Ta Bayyana Abinda Ya Yi Ajalinsa Hoto: Rotimi Akeredolu
Asali: Twitter

A wata sanarwa da kwamishinar yaɗa labarai ta jihar Ondo, Bamidele Ademola-Olateju, ta fitar, ta ce mutuwar mai girma gwamnan ta haifar da babban rauni a zuƙatan dukkan mazauna jihar.

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: An rantsar da sabon gwamnan Ondo bayan mutuwar Gwamna Akeredolu, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan, wanda ke jinya a ƙasar Jamus, ya amsa kiran Allah ne sakamakon cutar kansa watau ciwan dajin da ya shafa fama da ita.

Iyalai da gwamnati sun aika saƙo ga Tinubu

Bayanai sun nuna cewa tuni aka tura saƙon tabbatar da mutuwar gwamnan a hukumance ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Iyalan Gwamna Akeredolu da kuma gwamnatin jihar Ondo sun gode wa Shugaba Tinubu bisa goyon bayan da ya bayar a lokacin da mamacin ke jinya.

Kamar yadda sanarwan ta kunsa, iyalai da gwamnatin jihar zasu fitar da sauran bayanai kan yadda za a yi masa jana'iza da sauransu nan gaba kaɗan.

Kwamishinar ta ce:

"Gwamna ya bar duniya cikin kwanciyar hankali da sanyin safiyar yau Laraba, 27 ga Disamba, 2023. Wannan rashi ya bar mana gibi mai zurfi a cikin zukatanmu."

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bayyana ainihin silar mutuwar gwamnan APC, ta fadi babban halin gwamnan na kirki

"Gwamna Akeredolu ya amsa kiran Allah a lokacin da yake jinya a kasar Jamus. Ya rasu ne sakamakon ciwon kansa."
"Muna jin daɗi kuma hankalin mu ya kwanta idan muka tuna cewa Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu ya yi rayuwa mai ma’ana, mai sadaukar da kai ga bautar Allah."

Abinda ya faru a ofishin gwamnan Ondo bayan ya rasu

A wani labarin kuma kun ji cewa an nemi kowa an rasa a ofishin gwamnan jihar Ondo jim kaɗan bayan samun labarin Allah ya masa rasuwa a Jamus.

Rahotanni sun bayyana cewa kowa ya kama gabansa ya bar ofishin sauran jami'an tsaro ƙaɗai da aka bari suna gadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262