Fitaccen Malamin Musulunci Ya Faɗi Abinda Zai Faru da Bola Tinubu da Tsohon Ministan Buhari a 2024
- Malamin addinin Musulunci ya yi hasashen cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu da tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, zasu sasanta da juna
- Babban malami a Ilorin, Sheikh Sulaiman Farooq Onikijapa, ne ya yi hasashen a wurin addu'ar takwas ta marigayi Sheikh Abdulwahab Banni Afonta
- Onikijapa ya ce za a ɗauki lokaci kafin masalaha ta shiga tsakanin mutanen biyu amma ya jaddada yaƙinin zasu dawo zama a inuwa ɗaya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osogbo, jihar Osun - Alamu sun nuna shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da tsohon yaronsa a siyasa, Rauf Aregbesola, zasu shirya su sasanta kansu nan ba da jimawa ba.
Wani fitaccen malamin musulunci kuma jagora a Ilorin, Sheikh Sulaiman Farooq Onikijapa, ne ya yi wannan hasashen yayin da ake dab da shiga sabuwar shekara 2024.
Malamin ya ce dangantakar da ta yi tsami tsakanin shugaban ƙasa da tsohon gwamna jihar Osun kuma tsohon ministan cikin gida a mulkin Buhari zata zama tarihi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya hango ƙarshen rigimar Tinubu da tsohon ministan
Shehin Malamin ya jaddada cewa rigimar da ta shiga tsakanin jiga-jigan biyu zata ɗaukin dogon lokaci amma wata rana gaskiya zata yi halinta, Leadership ta ruwaito.
Onikijapa ya bayyana haka ne a wurin taron addu'ar takwas ta fidda'u da aka yi wa marigayi Sheikh Abdulwahab Banni Afonta, wani fitaccen malamin musulunci a Osogbo.
Taron addu'ar ya gudana ne a ɗakin taron Nelson Mandela Freedom Park da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun.
Sheikh Atonta, malami ne da ya taso daga Ilorin kuma ya samu wurin zama a Osogbo, inda ya shafe rayuwarsa ya gina makarantar larabci da masallaci.
Kotun Koli na shirin yanke hukunci kan zaben Kano, Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga Ganduje
Ya rasu ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, 2023 kuma an yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada washe gari ranar Lahadi.
Dalilin da ya sa Tinubu da Aregbesola zasu shirya
Sheikh Onikijapa ya kara da cewa Aregbesola ke wakiltar musulunci a siyasa kuma tsohon ministan bai taɓa musanta Tinubu a matsayin uban gidansa ba.
Malamin ya ce:
"Wani abu da na sani shi ne cewa za ka iya juya ƙarya ta koma gaskiya; babu mai iya juyar da gaskiya ta koma karya."
"Za a iya ɗaukar dogon lokaci, amma gaskiya za ta bayyana. Ina rokon Allah Ta’ala Ya gyara alakarku, ya dora ku a kan munafukai."
Idan baku manta ba, Aregbesola ya fara takun saƙa da Tinubu ne lokacin da ake zargin cewa ya ci amanar yunƙurin tazarce tsohon gwamnan Osun, Gboyega Oyetola.
Kotun koli na shirin kwace kujerar gwamnan APC
A wani rahoton na daban Ladi Adebutu ya bayyana kwarin guiwar cewa kotun koli zata kwace mulki daga Gwamna Abiodun, ta tabbatar masa da nasara.
Ɗan takarar gwamnan jihar Ogun a inuwar PDP a zaɓen 2023 ya faɗi haka ne a sakon kirsimeti da ya fitar ranar Litinin.
Asali: Legit.ng