"Tsoron Kotun Koli": Yan Najeriya Sun Yi Martani Bayan Gwamnan PDP Ya Yi Wa Tinubu Addu'a
- Gwamnan jihar Bauchi ya sha suka sosai sakamakon kalaman da ya yi a kan shugaban ƙasa Bola Tinubu
- Ƴan Najeriya sun caccaki gwamnan PDP Bala Mohammed a shafukan sada zumunta inda suka buƙaci shi da irin su, Nyesom Wike da su sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki
- Hakan na zuwa ne bayan Mohammed ya fito fili ya yi kira da a yi addu’a da goyon bayan gwamnatin tarayya da Tinubu ke jagoranta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya sanya mutane da yawa suna ta maganganu a shafukan sada zumunta kan wasu kalamai da ya yi.
Gwamnan ya buƙaci mabiya addinin Kirista da su yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’a domin samun nasara.
Kotun Koli na shirin yanke hukunci kan zaben Kano, Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga Ganduje
Mohammed, jigo a jam’iyyar PDP, ya yi wannan kiran ne a lokacin da al’ummar Kirista suka karrama shi a wani ɓangare na bikin Kirsimeti, a ranar Litinin, 25 ga watan Disamba a jihar Bauchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wacce addu'a Gwamna Bala ya yi wa Tinubu?
A cewarsa, nasarar Shugaba Tinubu a matsayinsa na jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), shi ma nasarar gwamnatinsa ce.
Ya ƙara da cewa irin wannan addu’a ya zama wajibi domin baiwa shugabanni damar gudanar da ayyukansu, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
"Ku manta da jam’iyyun siyasa amma ku yi wa shugaban ƙasa addu’a a matsayinsa na mutum kuma a matsayin shugaban ƙasa." A cewarsa.
"Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), da sauran shugabannin addinai su yi mana addu’a a matakai daban-daban na shugabanci."
Wannan na zuwa ne bayan kotun ƙoli ta tanadi hukunci a ƙarar da ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar APC, Sadique Baba Abubakar, ya shigar kan zaɓen gwamna Mohammed a ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba.
Wane irin martani ƴan Najeriya suka yi?
Ƴan Najeriya kamar yadda suka saba sun yi amfani da sashin sharhi na shafin X (tsohon Twitter) na jaridar tare da mayar da martani.
Ga kaɗan daga ciki nan ƙasa:
@muhamma03671918 ya rubuta:
"Tsoron kotun ƙoli ya sanya ya hankalta."
@olanipekunHenr3 ya rubuta:
"Kawai ka koma APC domin mu san makomar nasararka a matsayinka na gwamna tana tare da Tinubu."
@AadamMB ya rubuta:
"PDP ta yi saurin zama jam'iyyar adawa mara amfani."
@talk2heedman ya wallafa a Twitter:
"Cigaba shugaban PDAPC."
@SageEhis ya rubuta:
"Tuni ka gaza saboda Tinubu ya fara kan rashin nasara."
Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Bala
A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na jam'iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Bauchi.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar APC, Sadique Baba Abubakar ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Gwamna Bala a zaɓen gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng