Abin da Ya Sa Farin Jinin Bola Tinubu Yake Raguwa Tun da Ya Gaji Buhari, Jigon APC

Abin da Ya Sa Farin Jinin Bola Tinubu Yake Raguwa Tun da Ya Gaji Buhari, Jigon APC

  • Salihu Muhammad Lukman ya hira da manema labarai a kan tafiyar APC da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
  • Tsohon shugaban na APC a Arewacin Najeriya ya jero kura-kuren da ake samu bayan tafiyar Muhammadu Buhari
  • Alhaji Lukman wanda ya ajiye mukaminsa a APC bai goyon bayan yadda aka kawo Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Salihu Muhammad Lukman ya yi wata hira ta musamman, inda ya tabo batun siyasar Najeriya da jam’iyyarsa ta APC.

A tattaunawar da aka yi da shi a Tribune, Salihu Muhammad Lukman ya dauko batun alakarsa da Kwamred Adams Oshiomhole.

Bola Tinubu da Muhammadu Buhari
Bola Tinubu da Muhammadu Buhari Hoto: @OfficialABAT, @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Jam'iyyar APC na nan a gidan jiya?

Tsohon mataimakin shugaban na APC ya nuna ya yi mamaki da ya ji Abdullahi Umar Ganduje zai canji Abdullahi Adamu a NWC.

Kara karanta wannan

Kotun Koli na shirin yanke hukunci kan zaben Kano, Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga Ganduje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun nan Salihu Muhammad Lukman yake ganin an saba tsarin APC da mutumin Kano ya maye gurbin shugaba daga jihar Nasarawa.

Ko da Abdullahi Ganduje ya zama shugaban APC, Lukman ya ce babu taron da ake kira, ga shi an yi watsi da yankin Arewa ta tsakiya.

"Da farko na yi tunanin da zuwan Tinubu, za a samu bambanci sosai da yadda aka gudanar da gwamnati da jam’iyya a lokacin Buhari.
Na sa ran shugabannin jam’iyya za su rika aiki ta hanyar yin zama, kuma shugaban kasa zai amfana da shawarar manyan 'yan jam’iyya
...har jagororin jam’iyya su iya haduwa da shi, abin da aka rasa lokacin shugaba Buhari."

- Salihu Muhammad Lukman

Kuskuren da aka cigaba da yi a mulkin APC

Lukman yake cewa a tunaninsa, za a rika tattaunawa ana muhawara game da abin da kasa ke bukata a mulkin Bola Tinubu, amma ba ayi.

Kara karanta wannan

Yadda Abba Gida-Gida ya samu matsala, aka yi laifi wajen Rusau a Jihar Kano

Tun da aka canza gwamnati a watan Mayu, a hirarsa da jaridar, jagoran na APC ya nuna har yanzu abubuwa ba su canza zani a Najeriya ba.

Tsohon Darektan na kungiyar PGF ya koka a kan yadda aka daina maganar sauya fasalin kasa da yadda za a gyara tattalin arzikin Najeriya.

Farin jinin Bola Tinubu ya ragu ko ya karu?

A makonni biyun farko, Tinubu ya samu karbuwa sosai, amma Lukman ya ce sai abubuwa su ka soma yin kasa maimakon a cigaba a haka.

‘Dan siyasar ya ce lokaci bai kure ba, shugaban kasa zai iya canza lamarin kafin ayi nisa.

APC ta ba tsohon yaron Atiku mukami

Da aka tashi rabon darektoci, ana da labari Festus Keyamo ya tuna da tsohon mai taimakawa Atiku Abubakar watau Micheal Achimugu.

Mr. Achimugu ya yi aiki da Atiku Abubakar da yaransa kafin gwamnatin APC ta jawo shi cikinta bayan ya koma sukar ‘dan takaran na PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng