"Kada Ka Tsoma Baki a Kitimurmurar da Ke Tsakanin Abba da Gawuna a Kano", Dattijan Yarbawa ga Tinubu
- Shugaba Tinubu ya sha gargadi daga Yarbawa kan shari'ar Kano da za a yi nan ba da jimawa ba
- Kungiya ta ce ya koma gefe ya yi kallon abin da alkalai za su yanke, kada ya dauki matsayar jam'iyya
- Ana ci gaba da rikici da jiran hukunci tsakanin Abba Kabir Yusuf da Yusuf Gawuna a shari'a ta uku
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Kaduna - Kungiyar Yarbawa a jihar Kano, a ranar Asabar, ta gargadi shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya tsoma baki ga hukuncin da kotun koli ta tanada a shari'ar Abba Kabir Yusuf da Yusuf Gawuna.
ta kuma yi kira ga Ooni na Ife, Alaafin na Oyo, da Oba na Legas, da kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC, Cif Bisi Akande, da su yiwa Tinubu magana kan lamarin, Punch ta ruwaito.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da dattawan Yarbawa karkashin jagorancin Seyi Olorunsola suka fitar jim kadan bayan kammala taronsu a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin wannan kira ga Tinubu
Dattawan Yarbawa sun bayyana cewa rokon da suka yi wa Shugaban kasar ba wai ya na kada ya tsoma baki a shari'ar bane kadai, ya bari adalci ya yi aiki.
Har ila yau, sun gargadi shugaba Tinubu kan karkata zuwa ga tunani da kawazucin cewa APC ta rasa jihar Kano na iya kawo masa cikas ga siyasarsa.
Dattawan sun kuma yabawa bangaren shari’a kan matakin da suka dauka na tsayawa tsayin daka wajen bin doka da oda a hukuncin zaben gwamna.
Shari'ar Abba da Gawuna: Kallo ya koma sama a Kano
Ana ci gaba da cece-kuce da hasashen waye zai yi nasara a kotun koli tsakanin Abba da Gawuna, jama'a sun koma jiran tsammani.
A baya, an bayyana korar Abba Kabir Yusuf har sau biyu a zaman kotun kararrakin zabe da kuma na kotun daukaka kara.
Ya zuwa yanzu, an tanadi hukuncin da za a yanke, kuma ana ci gaba da jiran ranar da za a bayyana abin da alkalai suka yanke.
Asali: Legit.ng