Kano: Dattawan Yarbawa a Arewa Sun Yi Magana Kan Shari’ar Abba da Gawuna, Sun Tura Sako Ga Tinubu

Kano: Dattawan Yarbawa a Arewa Sun Yi Magana Kan Shari’ar Abba da Gawuna, Sun Tura Sako Ga Tinubu

  • Dattawan Yarbawa da ke Arewacin Najeriya sun bukaci a zauna lafiya yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli a jihar Kano
  • Dattawan sun ce ba za su tsoma baki a shari'ar jihar ba inda suka bukaci dukkan bangarorin biyu da su kai zuciya nesa
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Durojaiye Babalola ya fitar a yau Asabar 23 ga watan Disamba a Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiyar Dattawan Yarbawa da ke Arewacin Najeriya ta yi martani kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kano.

Dattawan suka ce ba za su tsoma baki a shari'ar ba amma sun bukaci dukkan bangarorin biyu da su kai zuciya nesa.

Kara karanta wannan

Shari’ar Kano: An shiga rudanin ‘wasikar’ da ake zargin Dahiru Bauchi ya rubutawa Alkalai

Dattawan Yarbawa a Arewa sun yi magana kan shari'ar Kano
Dattawan Yarbawa a Arewacin Najeriya sun magantu kan shari'ar Kano. Hoto: Nasiru Gawuna, Abba Kabir, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene kungiyar Yarbawa ke cewa kan shari'ar Kano?

Har ila yau, Kungiyar ta tabbatar da cewa dole kowa yabi hukuncin da Kotun Koli ta yanke ba tare da gardama ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta tabbatar da cewa zaman lafiya da fahimtar juna yafi komai muhimmanci a halin da ake ciki.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Durojaiye Babalola ya fitar a yau Asabar 23 ga watan Disamba a Kaduna, cewar Tribune.

Kungiyar ta tabbatar da irin gudunmawar da masarautun gargajiya ke bayarwa a cikin al'umma.

Wane bukata Yarbawan suka yi kan shari'ar Kano?

Ta kuma bukaci masu sarautar gargajiya na yankin Yarbawa kamar Ooni na Ife da Alaafin na Oyo da Oba na Legas su zauna da Tinubu kan hukuncin.

Sanarwar ta ce:

"Muna kira ga Shugaba Tinubu da kada ya shiga lamarin wannan hukunci na Kotun Koli, ya kamata ya bar kotu ta yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Ni na taimaki APC ta ci mulki, gwamnan Arewa ya soki 'yan Majalisar Tarayya da Suka Sako Shi a Gaba

"Ganin yadda mutanen Kano suka nuna matsayarsu a akwatunan zabe, Dattawan Yarbawa sun bukaci a bar wa mutane abin da suka zaba."

Dattawan suka ce ya kamata kowa ya mutunta duk wani hukunci da kotun ta yanke don dorewar zaman lafiya, cewar Newstral.

'Yan Kwankwasiyya sun ci gaba da azumi

A wani labarin, Yayin da ake ci gaba da dakon hukuncin Kotun Koli, 'yan Kwankwasiyya sun ci gaba da azumi.

Jam'iyyar tun farko ta bukaci magoya bayanta da su dauki azumi a ranar Alhamis don neman taimakon Allah a shari'ar.

Daga bisani, kotun ta tanadi hukunci kan shari'ar jihar inda ta ba da kafa don sanar da hukuncin nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.