Ni Na Taimaki APC Ta Ci Mulki, Gwamnan APC Ya Soki 'Yan Majalisar Tarayya da Suka Sako Shi a Gaba
- Yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Gwamna Alia da 'yan Majalisa, gwamnan ya yi martani
- Gwamna Hyacinth ya soki 'yan Majalisar da kaucewa tafarkin gina al'umma inda suka koma neman kushe tsarin mulkinsa
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Tersoo Kula ya fitar a yau Juma'a 22 ga Disamba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya yi martani kan zargin da 'yan Majalisar jihar ke yi a kansa.
'Yan Majalisar na zargin gwamnan da kama-karya a jihar tun bayan hawanshi karagar mulki.
Mene Gwamna Alia ya ce kan zargin?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Tersoo Kula ya fitar a yau Juma'a 22 ga Disamba, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kula ya ce kasancewar Alia a APC shi ya ba ta damar samun nasara a babban zabe da aka gudanar a farkon wannan shekara.
'Yan Majalisar da ke Tarayya sun soki tsarin mulkin Alia inda su ka ce ya yi watsi dasu a harkokin gudanar da mulkinsa.
Wace shawara gwamnan ya bai wa 'yan Majalisun?
Sai dai Kula ya zargi 'yan Majalisun da watsi da mutanen yankinsu inda suka koma nemo hanyar bata wa gwamnan suna, cewar TheCable.
Ya shawarce su da su nemo hanyar inganta rayuwar wadanda suka zabe su madadin mayar da hankali a mulkin Gwamna Alia.
Tersoo ya ce Gwamna Alia ya ba da gudunmawa wurin tabbatar da nasarar APC a babban zaben da aka gudanar.
Ya kuma yi fatali da zargin cewa gwamnan bai tabuka abin a zo gani ba jihar tsawon watannin da ya ke mulki a jihar.
'Yan Majalisa sun saka wando daya da Gwamna
A wani labarin, An shiga takun saka tsakanin Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue da 'yan Majalisun Tarayya.
'Yan Majalisar Tarayya daga jihar na kalubalantar gwamna da zargin cewa ya na gudanar da mulkin kama-karya a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan 'yan Majalisar sun soki gwamnan da rushe ciyamomin kananan hukumomi.
Asali: Legit.ng