“Yadda Tinubu Ya Tursasa Gwamnan Ribas Sa Hannu a Yarjejeniya da Karfin Tsiya a Aso Villa”

“Yadda Tinubu Ya Tursasa Gwamnan Ribas Sa Hannu a Yarjejeniya da Karfin Tsiya a Aso Villa”

  • David Briggs ya yi magana da manema labarai a game da rikicin siyasar da sulhun da aka yi a jihar Ribas
  • Tsohon kwamishinan ya ce da su aka je wajen taron, kuma barazana shugaban Najeriya ya yi wa Simi Fubara
  • A cewar Briggs, Bola Tinubu ya nuna zai dauki mataki idan Gwamnan Ribas ya ki amincewa da yarjejeniyarsa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Rivers - David Briggs tsohon kwamishinan ayyuka ne a jihar Ribas, ya yi bayani game da yarjejeniyar sulhun siyasar da aka yi.

Cif David Briggs a wata hira da aka yi da shi, ya shaidawa Channels barazana aka yi wa Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa.

Shugaban kasa da Gwamnan Ribas
Shugaban kasa ya tursasa Gwamnan Ribas Hoto: @OfficialABAT/@SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya yi wa Gwamna barazana

Kara karanta wannan

Sabon rikici zai kurdo jam’iyyar PDP, Atiku ya lula Dubai bayan shari’ar zabe

David Briggs ya yi ikirarin ya halarci taron, ya ce da karfi da yaji aka samu Mai girma gwamnan jihar Ribas ya sa hannu wajen sulhun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon kwamishinan ya halarci zaman da aka yi a makon nan, ya nuna ba don gwamnan Ribas ya so, ya amince da yarjejeniyar ba.

Matsin lamba Fubara ya sha wajen Tinubu?

Shi dai kwamishinan yada labarai na jihar Ribas, Joseph Johnson ya ce ba matsawa mai gidansa aka yi sa hannu a wajen taron ba.

Joseph Johnson ya nuna Gwamna Simi Fubara ya amince da hakan ne a kan zabin kan shi saboda kowa ya zauna lafiya a jihar Ribas.

Da aka yi hira da Briggs a ranar Alhamis, Vanguard ta ce ya tabbatar da cewa yana cikin wadanda aka gayyata, ya ga komai da idonsa.

Kara karanta wannan

"Kudin ka mutuncin ka", Dino Melaye ya ba 'yan Najeriya shawarar su tashi su nemi arziki

Abin da David Briggs ya fada

"Ina wajen, saboda haka abin da na fada ganau ne, ba labari aka ba ni ba. An gayyace mu taro, amma ba taro aka yi ba.
Abin da ya faru shi ne shugaban kasa ya shigo da rubutacciyar takarda, ya yi mana jawabi.
Sai (Bola Tinubu) ya fada mana abin da ke hannunsa kudirin shugaban kasa ne, kuma yana da ikon ladabarwa.
Ya nanata cewa shi ne shugaban tarayyar kasar Najeriya, kuma duk wanda ya saba masa zai gamu da tasirin hakan."

- David Briggs

Dattijon ya ce ba Tinubu ya karanto takardar ba, ya mikawa Peter Odili ne ya karanta.

Shugaba Tinubu zai sasanta Wike da Fubara

An ji labarin yadda Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya kira zaman sulhu a fadar Aso Rock Villa a kan rigimar siyasar jihar Ribas.

Tun tuni Shugaban kasa yake ta kokarin kawo karshen sabanin da ke tsakanin Siminalayi Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel