Kano: Yayin da Aka Tanadi Hukuncin Shari'ar, 'Yan Kwankwasiyya Sun Zarce da Azumin Neman Nasara
- Magoya bayan jam'iyyar NNPP a jihar Kano sun bi umarnin jami'yyar yayin da ake hukuncin Kotun Koli kan shari'ar zaben jihar
- Jam'iyyar tun a jiya ta bukaci magoya bayanta su tashi da azumi a yau Alhamis 21 ga watan Disamba don samun nasara
- A yau Alhamis ce aka yi zaman kotun inda ta tanadi hukunci don ba da hukuncin karshe a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da Kotun Koli ta tanadi hukunci a shari'ar zaben jihar Kano mafi yawan magoya bayan jam'iyyar NNPP sun dauki azumi.
Jami'yyar ta yi ta kiran magoya bayanta da su tashi da azumi a yau Alhamis 21 ga watan Disamba don neman nasara.
Wane hukuci kotun ta yanke?
Daily Trust ta tattaro cewa a yau Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar da ya dauki hankulan 'yan kasar baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane da dama sun bi umarnin inda su ke yin azumin tare da addu'o'i gabannin hukucin.
Daraktan yada labarai na jami'yyar, Sunusi Bature ya ce tabbas mafi yawan magoya bayansu sun dauki azumin.
Wane hukunci aka yi a baya?
Har ila yau, an ci gaba da kiran jama'a da su ci gaba da azumin da Addu'o'i har bayan zaman kotun, cewar TheCable.
Wannan na zuwa ne yayin dan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna na kalubalantar zaben Gwamna Abba Kabir a jihar.
Kotun zaben da ta Daukaka Kara duk sun rusa zaben Gwamna Abba Kabir saboda kura-kurai da ke tattare da zabenshi.
Kotu ta tanadi hukunci a shari'ar zaben Kano
A wani labarin, yayin da zaman dar-dar kan hukuncin zaben jihar Kano, Kotun Koli ta tanadi hukunci.
A yau Alhamis 21 ga watan Disamba ce aka yi zaman kotun wanda ya dauki hankulan 'yan kasar baki daya.
Daga bisani kotun ta yi hukuncin inda ta sake ba da kafa kan raba gardama a shari'ar tsakanin Abba Kabir da Nasiru Gawuna.
Asali: Legit.ng