An Saurari Karar Abba, Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci a Shari’ar Gwamnan Jihar Kano

An Saurari Karar Abba, Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci a Shari’ar Gwamnan Jihar Kano

  • Nan da 'yan kwanaki za a san wanda ya yi nasara a shari'ar da ake yi a kan zaben Gwamnan Kano
  • Alkalai biyar su ka zauna a teburin kotun koli domin raba gardama a shari’ar da aka fara tun Afriku
  • Inyang Okoro wanda ya yi hukunci a shari’ar Bola Tinubu da PDP a zaben 2023 ya jagoranci zaman

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kotun koli ta kammala sauraron karar Abba Kabir Yusuf da ya daukaka a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano.

Rahoton da mu ka samu daga Daily Trust ya tabbatar da cewa kotun koli ta tsaida lokacin da za a yanke hukunci a karar.

Nasir Gawuna
Shari’ar Gwamnan Kano a Kotun koli Hoto: @KyusufAbba da @NasirGawuna
Asali: Twitter

Inyang Okoro za su yi hukunci a zaben Kano

Kara karanta wannan

Abin da ya faru tsakanin Lauyoyin Abba, NNPP, INEC da Lauyan APC a Kotun Koli yau

Alkalai biyar su ka saurari shari’ar a karkashin jagorancin Mai shari’a Inyang Okoro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara a sakamakon hukuncin kotun daukaka da ta tsige shi bayan INEC ta ba shi nasara.

Moore A. Adumein ya zartar da cewa Nasir Yusuf Gawuna ne ya yi nasara domin NNPP ba ta da ‘dan takara a Kano.

Lauyoyin NNPP sun kare zaben Abba

Lauyoyin Abba Kabir Yusuf sun fadawa kotun koli babu dalilin soke nasarar Abba Kabir Yusuf saboda kuskuren INEC.

Kotunan da su ka saurari shari’ar zaben gwamnan Kano a baya sun soke kuri’u 160, 000 da sunan ba halatattu ba ne.

Abba Hikima wanda lauya ne mazaunin Kano, ya ce duk alamu sun nuna alkalan kotun kolin za su yi a adalci a shari'ar.

Yaushe za ayi hukunci kan zaben Kano?

Kara karanta wannan

‘Yan Kwankwasiyya, Masoyan Abba sun tashi da azumi domin yin nasara a Kotun koli

Kafin yanzu an yi ta rade-radin cewa a yau za a yanke hukunci bayan an gama sauraron ta bakin lauyoyin APC da na NNPP.

Sai nan gaba kadan kotun koli za ta sanar da wadanda ake shari’ar da su lokacin da za a yanke hukuncin da zai zama na karshe.

APC da NNPP na addu'ar nasara a Kano

Kafin a fara shari’ar, alkalan kotun kolin sun ce za su iya yin kuskure, sai dai babu damar da wani zai iya daukaka kara a doka.

Alhassan Ado Doguwa ya yi magana a shafin X, ya ce suna fatan nasara kamar yadda magoya bayan NNPP ke ta faman addu’a.

...'Yan Kwankwasiyyan Kano sun dauki azumi

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bada sanarwa cewa magoya bayan Abba Kabir Yusuf su dauki azumi saboda zaman kotun da za ayi.

Ana ganin abubuwa iri-iri a siyasar Kano domin wasu sun kawo wata sallar mutum miliyan guda saboda a soke nasarar APC a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng