Jerin Manyan 'Yan Siyasa da Sauya Shekarsu Ta Girgiza Siyasar Najeriya a 2023
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Siyasar Najeriya ta fuskanci gagarumin sauyi a 2023, sakamakon abubuwa da dama da suka faru. A wannan lokacin kuma, an samu bayyanan sabbin jam'iyyun siyasa da suka sauya yanayin siyasar kasar.
Kafin shekarar 2023, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ne suka mamaye siyasar Najeriya.
Zuwa wani lokaci, yan siyasa sun koma wasu jam'iyyun domin cimma kudirinsu na yin takara bayan sun ga irin barazanar da suke fuskanta a jam'iyyunsu na siyasa, wannan ne dalilin da yasa sauyin sheka ya zama ruwan dare.
Ga jerin wasu da suka yi jawabai masu karfi yayin da suka sauya sheka a 2023 a kasa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabiu Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano yana daya daga cikin wadansa suka yi jawabai masu zafi bayan ya bar jam'iyyar PDP tare da yin takara a jam'iyyar NNPP.
Tun bayan da ya koma NNPP, wacce aka kafa kafin zaben shugaban kasa na 2023, Kwankwaso ya zama idon NNPP. Wannan ci gaban ya haddasa takaddama a jam'iyyar a baya-bayan nan, inda mambobin jam'iyyar suka yi kokarin nuna cewa ba shine ya kafa jam'iyyar ba.
Sai dai kuma, Kwankwaso ya taka muhimmiyar rawar gani a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu inda ya samu kuri'u 997,279 a jihar Kano, yana mai kayar da Shugaban kasa Bola Tinubu na APC da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na PDP a jihar.
Peter Obi
Sauya shekar Obi daga PDP zuwa LP na daya daga cikin sauyin sheka da suka girgiza siyasar Najeriya a 2023.
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasar na PDP a zaben 2019 ya yi yunkurin bayan ya gane cewa ba lallai ne ya zama dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa ba.
Tafiyar 'Obideint' na Peter Obi ya yi karfi a babban zaben ta yadda ya shafi manyan yan siyasa da dama tare da shigo da sabbin fuskoki da dama cikin siyasar Najeriya.
A zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, Obi ya zama babban barazana ga Tinubu da Atiku sannan ya samu kuri'u fiye da miliyan shida.
Alex Otti
Wani labarin sauyin sheka da ya bayyana a zaben 2023 shine na Alez Otti da ya bar APC ya koma LP a jihar Abia. Ya koma jam'iyyar LP tare da shugaban APC a jihar Abia.
Gwamnan na jihar Abia a yanzu ya yi takarar tikitin gwamnan jam'iyyar APC mai mulki amma ya sha kaye. Jim kadan bayan nan ya koma LP, ya yi takara sannan ya lashe zaben gwamnan jihar.
Sanata Ifeanyi Ubah
Sanata mai wakiltan Anambra ta kudu ya sanar da sauya shekarsa daga jam'iyyar YPP zuwa APC a zauren majalisar dattawa.
A cikin wasikarsa zuwa ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, dan siyasar na Anambra ya bayyana rikcin da ya dabaibaye jam'iyyar YPP a matsayin dalilinsa na sauya sheka.
Baya ga komawa APC daga jihar Peter Obi, an zabi Ubah a matsayin sanata sau biyu a karkashin jam'iyyar YPP.
Yan siyasar da suka yi asara a 2023
A wani labarin, mun ji cewa fitattun ‘yan siyasa bila-adadin ba su samu yadda su ke a zaben da aka yi a shekarar nan ba, amma akwai wanda rashinsu ya fi zafi. Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp.
Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi! Rahotonmu ya tattaro jerin ‘yan siyasan da su ka shiga takara ko aka sa ran za su samu mukami a gwamnati, amma su ka tashi babu komai.
Asali: Legit.ng