Kano: Daga Karshe Ganduje Ya Yi Magana Kan Hukuncin Kotu a Shari'ar Zaben Doguwa

Kano: Daga Karshe Ganduje Ya Yi Magana Kan Hukuncin Kotu a Shari'ar Zaben Doguwa

  • An bayyana ɗan majalisar wakilai na jam'iyyar APC, Alhassan Ado Doguwa a matsayin wata kadara ta siyasa
  • Doguwa ya samu yabo ne daga shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje
  • Ganduje ya yaba masa bisa samun nasara a ƙarar da ke neman a kore shi a matsayin ɗan majalisar wakilai ta ƙasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan nasarar da Alhassan Ado Doguwa, ya samu a kotu.

Ganduje ya ce nasarar da Doguwa ya samu a kotun ɗaukaka ƙara wanda shi ne shugaban ƙungiyar ƴan majalisar wakilai na Arewacin Najeriya, ta tabbatar da zaɓin jama’a, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta kasa ta yi wa Shugaba Tinubu da CBN babbar barazana kan abu 1 tak

Ganduje ya taya Doguwa murna
Ganduje ya taya Alhassan Doguwa murnar nasara a kotun daukaka kara Hoto: Dr Abdullahi Umar Ganduje, Alhassan Ado Doguwa
Asali: Facebook

A wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Edwin Olofu, Ganduje ya ce hukuncin kotun ya tabbatar da cewa mazauna mazaɓar tarayya ta Tudun Wada/Doguwa sun goyi bayan Doguwa da gaske a zaɓen da ya gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane irin yabo Ganduje ya yi wa Doguwa?

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya bayyana Doguwa a matsayin ƙwararre kuma ɗan siyasa mai son al’umma wanda ya samu karɓuwa ta hanyar gudunmawar da ya daɗe yana bayarwa, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Gandjue ya yabawa Doguwa a matsayin wakilin mazabarsa mai ƙima, inda ya jaddada ƙwarewarsa a fannin dokoki da yi wa sauran ƴan majalisar zarra, da kyakkyawan tasirinsa ga Kano da ƙasa baki ɗaya.

A kalamansa:

"Doguwa wata kadara ce da kowa ke son ya samu. Mun yi murna kuma mun gamsu da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta tabbatar da zaɓensa. Muna masa fatan alheri, muna taya shi murna”.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan yarjejeniya 8 da Tinubu ya cimmawa tsakanin Wike da Fubara

Tsohon gwamnan na Kano ya yabawa ɓangaren shari’a bisa wannan gagarumin hukunci.

Ganduje Ya Yi Nadin Mukamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi naɗin muƙamai.

Ganduje ya naɗa nada wanda zai zama shugaban ma’aikata a ofishinsa, inda ya naɗa Malam Muhammaɗ Garba a wannan muƙamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng