Natasha, Ireti da Sauran Manyan Yan Siyasa Mata da Tauraruwarsu ta Haska a 2023
- Yanayin siyasar Najeriya a 2023 ya cika da ɗimbin abubuwan kallo da za a iya kwatanta su da Hollywood
- A siyasar da aka buga a zaɓen 2023 an ga abubuwan mamaki sosai da aka daɗe ba a gansu ba a ƙasar nan
- A zaɓen na 2023, ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka fii ɗaukar hankali shi ne yadda wasu tsirarun mata suka kayar da maza a wasu kujerun siyasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - A fagen siyasar Najeriya, zaɓukan shekarar 2023 sun zama mahanga wacce ta nuna an fara samun cigaba wajen daidaito a siyasar ƙasar nan.
Kamar yadda sakamakon ya bayyana, wani gagarumin al'amari da ya zama abun magana shi ne yadda mata suka samu nasara a wasu kujerun siyasa.
Duk da kasancewar zaɓen a matsayin wanda mata ba su yi takara ba sosai a cikinsa, wasu daga cikinsu sun yi abin da ba a yi tsammani ba inda suka lashe zaɓen su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng ta tattaro matan da suka zama zakaran gwajin dafi a zaɓen 2023.
1. Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
Sanata Natasha ta fito a matsayin fitacciyar mace a zaɓen da aka gudanar a baya bayan nan, inda ta shiga takarar neman kujerar Sanatan Kogi ta tsakiya a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP.
Duk da cewa tunda farko INEC ta bayyana Abubakar Ohere na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen, kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke sakamakon a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, inda ta soke nasarar Ohere tare da tabbatar da Natasha a matsayin wacce ta lashe zaɓen.
Ganin manyan nasarorin da ta samu, Natasha ta sami lambar yabo ta "Gwarzuwar ƴar siyasa ta shekarar 2023" wacce Leadership ta bayar.
2. Sanata Ireti Heebah Kingibe
Sanata Ireti Kingibe daga jam’iyyar Labour Party ta kafa tarihi a babban birnin tarayya Abuja inda ta kayar da Sanata Phillip Aduda na jam’iyyar PDP wanda ya yi wa’adi uku a zaɓen 2023, lamarin da ya karya ƙarfin mazaje a siyasar FCT.
A zaɓen 2023, jami’in zaɓe na INEC, Sanni Saka, ya sanar da cewa Ireti ta samu ƙuri’u 202,175, inda ta samu nasarar lashe zaɓen, yayin da Philip Aduda na PDP ya zo baya da ƙuri’u 100,544.
Angulu Dobi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu matsayi na uku da ƙuri’u 78,905.
Musamman ma, Sanata Ireti mai shekaru 69, kanwar Ajoke Muhammed ce, matar tsohon shugaban Najeriya Murtala Muhammed.
3. Hon Rukayat Motunrayo Shittu (RMS)
Rukayat Motunrayo Shittu tana da shekaru 26 a duniya, wacce ta kammala karatun digiri na biyu a jami’ar NOUN, da jajircewa ta shiga fagen siyasa inda ta tsaya takara a mazabar Owode/Onire da ke ƙaramar hukumar Asa a majalisar dokokin jihar Kwara.
Shittu ta shiga neman kujerar ƴar majalisa a majalisar dokokin jihar Kwara, inda ta tsaya takara a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana Rukayat Shittu a matsayin wacce ta lashe zaɓen da ƙuri’u 7,521, inda ta doke Abdullah Magaji na jam’iyyar PDP, wanda ya samu ƙuri’u 6,957.
Bayan rantsar da ita a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, Rukayata ta kafa tarihi a matsayin ƴar majalisa mafi ƙarancin shekaru a jihar.
4. Idiat Oluranti Adebule Idiat
Oluranti Adebule ta riƙe mukamin Sanata mai wakiltar Legas ta yamma bayan nasarar da ta samu a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Idiat ta yi nasara a kan Segun Adewale, wanda ya tsaya takarar a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP. Idiat ta samu ƙuri’u 361,296 inda ta doke Adewale wanda ya samu ƙuri’u 248,653.
Kafin aikin da take yi a yanzu, ita ce mataimakiyar gwamnan jihar Legas ta 15, inda ta zama mace ta shida da ta hau wannan muƙamin, inda ta yi aiki daga shekarar 2015 zuwa 2019.
"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya
5. Ipalibo Gogo Banigo
Ipalibo Gogo Banigo, kwararriyar likita ce kuma ƴar siyasa, a halin yanzu tana riƙe da muƙamin sanata mai wakiltar mazabar Rivers ta Yamma.
Harry-Banigo, wacce ta tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ta yi nasara inda ta doke tsohon shugaban hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA, Hon. Asita, wanda ta kasance ɗan takarar APC.
Kafin ta zama sanata, ta yi aiki a matsayin mace ta farko da ta zama mataimakiyar gwamnan jihar Rivers ƙarƙashin tsohon gwamna Nyesom Wike daga 2015 zuwa 2023.
Mata Mataimakan Gwamnoni a Najeriya
A wani labarin kuma, mun tattaro muku jerin ƴan siyasa mata waɗanda ke riƙe da muƙaman mataimakan gwamna a Najeriya.
A zaɓen 2023 an samu mata takwas waɗanda suka samu muƙamin mataimakin gwamna a faɗin ƙasar nan. Daga cikin su akwai Hadiza Balarabe ta jihar Kaduna da Kaleptawa Farauta ta jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng