2023: Fitattun mata 'yan siyasa 6 da ake sa ran zakarunsu zasu yi cara babu dadewa

2023: Fitattun mata 'yan siyasa 6 da ake sa ran zakarunsu zasu yi cara babu dadewa

- A kasar nan, matan da ke shiga siyasa basu da yawa kuma har yanzu tsiraru ne

- Tuni dai ake ta tattaunawa a kan yadda za a fadada yawan mata da ke siyasa a Najeriya

- Amma kuma duk da haka, akwai matan da suka tashi tsaye inda suke yin suna a cikin maza 'yan siyasa

Siyasar Najeriya kwata-kwata ba ta mata bace saboda basu kai labari. Hakan ya matukar shafan yawan matan da ke zama zakaru a siyasar kasar nan.

Amma kuma duk da hakan akwai matan da suka jajirce suna aiki tamkar maza wanda hakan yasa ake ganin za su kai labari a siyasa.

Legit.ng ta tattaro muku zakakuran mata 6 'yan siyasa a Najeriya da suka dage kuma alamu na nuna zasu yi suna a siyasance nan da 2023.

KU KARANTA: Umarnin Ubangiji ne: Fasto yayi zanga-zanga kan mulkin Buhari da akwatin gawa

2023: Fitattun mata 'yan siyasa 6 da zasu bada mamaki yayin zabe
2023: Fitattun mata 'yan siyasa 6 da zasu bada mamaki yayin zabe. Hoto daga @hadizabalausman
Asali: UGC

KU KARANTA: Sojan ruwa ya sokawa sojan sama wuka bayan ya kama shi turmi da tabarya da matarsa

1. Senator Abidoun Olujimi

'Yar siyasa ce kuma tsohuwar gwamnan jihar Ekiti wacce ta zama abun koyi sakamakon gogewarta a siyasa.

Olujimi ta samu sunanta ne tun lokacin da tayi aikin jarida kafin ta fada harkar siyasa dumu-dumu. A halin yanzu ita ke wakiltar mazabar Ekiti ta kudu a majalisar dattawa. Za ta nemi kujerar gwamnan jiharta a zaben 2022.

2. Senator Aishatu Dahiru Ahmed

An fi saninta da Binani kuma tana wakiltar mazabar Adamawa ta tsakiya ne a majalisar dattawa. Ta shiga siyasar kasar nan ne a 2015 kuma tuni tayi suna. Ko kafin shiganta siyasa, Binani ta yi suna a duniyar kasuwancin Najeriya.

3. Natasha Akpoti

Matashiyar 'yar siyasan mai shekaru 41 ta nemi kujerar sanata ta Kogi ta tsakiya da kuma ta gwamnan jihar karkashin SDP, zabukan da duk ta sha kaye.

Duk da kayen da ta sha, dole ne a kira ta 'yar siyasa maras tsoro tare da jajircewa wacce za ta iya jan hankulan mutane tun daga tushe.

4. Gbemi Saraki

A shekarunta na 55, tana biye sau da kafa da yanayin siyasar mahaifinta Olusola da dan uwanta Bukola, wadanda suka kasance fitattun 'yan siyasa a Najeriya.

Ita ce karamar ministan sufuri kuma tsohuwar sanata da ta wakilci Kwara ta tsakiya a 2003. Ana tsammanin sake bayyanar siyasarta a 2023.

5. Senator Uche Ekwunife

A shekarunta na 50 kacal, Sanata Ekwunife ta yi nisa a siyasarta inda ta tsallaka har ta kai majalisar wakilan Najeriya.

Ekwunife za ta samu damar baiwa masu tantama mamaki nan da 2023 inda take neman tikitin takarar kujerar gwamnan jihar Anambra a 2021.

6. Hadiza Bala Usman

Matashiyar mai shekaru 45 'yar siyasa ce kuma ita ce manajan daraktan hukumar mashigan ruwa ta Najeriya.

A baya ita ce shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2016.

Duk da matsayinta a halin yanzu, ta cigaba da gwagwarmayar siyasarta karkashin jam'iyyar APC inda ake fatan zakaran zai yi cara a 2023.

A wani labari na daban, lamari ya dauka zafi tsakanin wasu 'yan kwamitin rikon kwarya na majalisar wakila a kan makamai, da shugaban sojin kasa, Laftanal janar Ibrahim Attahiru bayan bincike a kan siyan makamai na sojin Najeriya.

Lamarin ya juya yayin da shugaban sojin kasan ya ki kara bayani kan wasu takardu da ya mika gaban kwamitin inda yace su duba takardun da kansu domin babu wani karin bayani.

Shugaban sojin ya jaddada cewa bai dade da hawa kujerarsa ba don haka ba shi ke da hakkin yin magana a kan makaman da magabatansa suka siya ba, Channels Tv ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel