Ko Yanzu Za a Sake Zabe APC Ce Da Nasara a Kano, Dan Takarar Sanata a Jihar Ya Tona Asirin NNPP
- Jigon jam’iyyar APC a Kano ya bayyana abin da zai faru a jihar idan da za a sake zabe ko a gobe ne
- Abdulkarim Zaura ya ce wadanda su ka zabi NNPP a yanzu haka su na dana sani kuma sun dawo daga rakiyarsu
- Zaura wanda ya yi takarar sanata a Kano ta Tsakiya ya ce ko yanzu jam’iyyar APC ce za ta yi a zabe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Dan takarar sanata a mazabar Kano ta Tsakiya, Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya ce ko an sake zabe APC ce za ta yi nasara.
Zaura wanda ya yi takara a jam’iyyar APC a wannan shekara ya bayyana cewa jam’iyyar ce za ta yi nasara idan da za a sake zabe yanzu a Kano.
Mene jigon APC ke cewa kan zaben Kano?
Dan takarar ya bayyana haka ne ga manema labarai a Abuja inda ya ce mutanen da su ka zabi NNPP a yanzu haka su na dana sani, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa dalilin samun matsalar APC a yankin Arewa maso Yamma bai rasa nasaba da sauya fasalin naira da kuma tsadar man fetur a kasar.
Abdulkarim ya ce wahalhalun da matakan APC su ka jefa jama’a shi ya saka su watsar da jam’iyyar inda NNPP ta samu galaba, cewar Leadership.
Yayin da ya ke magana kan sauya fasalin naira Zaura ya ce rashin wadatattun kudade a kasa ya jefa mutane cikin mummunan yanayi a wancan lokaci.
Ya ce:
“Bankin CBN ya sauya launin takardar naira, lokacin da aka sauya launin an samu karancin kudaden a hannun al’umma.
“Ka na da naira dubu 100 ko dubu 20 a asusun bankinka amma ba ka da damar yin amfani da su don ciyar da kanka.”
Ya kara da cewa:
“Ina da tabbaci a Kano idan za a sake zabe gobe, APC ce za ta yi nasara, babu jam’iyyar da za ta yi nasara kan APC.
“Dukkan mutanen da su ka zabi NNPP yanzu haka su na dana sanin haka saboda sun gane kuskurensu ne bayan an sanar da sakamakon zabe.”
APC ta yi martani kan yarjejeniya da NNPP
A wani labarin, jam'iyyar APC ta karyata jita-jitar cewa sun kulla yarjejeniya da NNPP a Kano kan shari'ar zabe.
Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli a ranar Alhamis 21 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng