Duka Yarjejeniya 8 Da Aka Dauka Wajen Sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock
- Bola Ahmed Tinubu ya tsoma baki a karo na biyu domin a magance sabanin siyasar da ake fama da ita a jihar Ribas
- Shugaban Najeriya ya bada umarni a dauki matakai 8 da ake sa ran za su dinke barakar Simi Fubara da Nyesom Wike
- Idan aka bi umarnin, za a ajiye magana tsige gwamnan Ribas kuma Wike da mutanensa za su samu yadda su ke so
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakanin Gwamna Simi Fubara da Nyesom Wike a rikicin siyasar da ake yi a jihar Ribas.
Tashar NTA ta rahoto cewa an cin ma yarjejeniya a taron da aka yi ranar Litinin a fadar shugaban kasa domin kawo karshen matsalar.
Rikicin Ribas: Yadda aka yi taron sulhu a Aso Rock
Manyan jami’an gwamnati, ‘yan siyasa da kusoshin PDP da APC sun halarci zaman, kuma a karshe su ka rattaba hannu kan yarjejeniyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu da shugaban APC na riko a Ribas, Tony Okocha sun sa hannu a takarda.
Daily Trust ta ce Nyesom Wike wanda yake fada da magajinsa a jihar Ribas ya iso wajen taron da kimanin karfe 7:00 na yammacin jiya.
Jerin yarjejeniya 8 da Wike-Fubara suka amince da su
- A janye duk wani yunkurin tunbuke Gwamnan jihar Ribas ba tare da bata lokaci ba.
- A gaggauta janye duk wata karar da gwamnan Ribas, Simi Fubara ya shigar a kotu a kan rikicin siyasar jihar.
- A yarda da jagorancin Rt. Hon. Martin Amaewhule a matsayin shugaban majalisar tare da mutane 27 da su ka bar PDP.
- Dole ayi gaggawan cigaba da biyan duk wasu hakkokin ‘yan majalisar dokoki kuma gwamna ya daina tsoma masu baki.
- Majalisar dokokin Ribas ta zabi inda ta ke so ta zauna domin aiki ba tare da katsalandan daga bangaren zartarwa ba.
- Mai girma gwamnan Ribas ya sake gabatar da kundin kasafin kudin 2024 a gaban daukacin ‘yan majalisar dokoki.
- A sake gabatar da sunayen Kwamishinonin da su kayi murabus zuwa ga majalisa domin a sake amincewa da su.
- Ka da a kafa kwamitin rikon kwarya na kantomomi a Ribas, tsige shugabannin kananan hukumomi ya sabawa doka.
An kawo karshen rikicin Ribas?
Ana da labari cewa Nyesom Wike, Simi Fubara, Martin Amaewhule da Aaron Chukwuemeka sun je taron kuma sun sa hannu.
Kashim Shettima, Femi Gbajabiamila, Farfesa Ngozi Ordu da Peter Odili su na cikin wadanda aka yi zaman da su a fadar Aso Rock.
Asali: Legit.ng