An Bankado Wata Kullalliya da Gwamnatin Tinubu Take Yi Wa Peter Obi

An Bankado Wata Kullalliya da Gwamnatin Tinubu Take Yi Wa Peter Obi

  • Wata hira da Peter Obi yayi kwanan nan ta sanya mutane da yawa suna magana a shafukan sada zumunta, musamman a Twitter
  • A cikin hirar, Obi ya yi magana kan takararsa ta shugabancin ƙasa a 2023 da kuma barazanar da yake samu a yunƙurinsa na samar da ingantacciyar Najeriya
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya yi nuni da cewa an yi masa barazana ne saboda ya ƙi amincewa da tayin da zai hana shi sukar gwamnatin Shugaba Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Peter Obi, ɗan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya caccaki gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu da sabon zargi.

Da yake magana a wata tattaunawa a shafin Twitter, Parallel Facts, Obi ya bayyana cewa ana yi masa barazana saboda ya fito fili yana sukar gwamnatin APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fara tunanin ɗauko tsohon ministan Buhari ya maye gurbin Lalong, ya gana da jiga-jigai 2

Ana son hana Peter Obi sukar gwamnatin Tinubu
Ana zargin gwamnatin Tinubu da yi wa Peter Obi barazana Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sai dai ya cigaba da cewa bai girgiza ba kuma ba zai daina sukar ba har sai an samar da sabuwar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana hakan a cikin wani saƙon da wani mai amfani da Twitter @TheOfficialPOMA ya sanya a ranar Lahadi, 1 ga watan Disamban 2023.

POMA ya rubuta a Twitter cewa:

"Mai girma Peter Obi ya yi tsokaci kan shirin musguna masa ko rufe baki da gwamnatin Tinubu ta yi."
"Ƴan Najeriya suna kallo."

Sowore ya faɗi taimakon da ya yi wa Peter Obi

Tun da farko kun ji cewa Omoyele Sowore ya yi bayanin cewa shi ne ya sanya Peter Obi ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), a zaɓen 2023.

Yayin da yake musanta cewa ya damu da Obi, Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar AAC, ya ce ba shi ne karon farko da zai taimakawa tsohon gwamnan ba.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Wike ya aike da muhimmin gargadi ga Gwamna Fubara

Peter Obi Ya Je Ta'aziyya a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi, ya roƙi gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike kan kuskuren jefa bam a kauyen Tudun Biri.

Ɗan takarar na shugaban ƙasar na jam'iyyar Labour Party (LP) ya bayyana hakam ne bayan ya kai ziyarar jaje ga waɗanda harin ya shafa a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel