Kotu Ta Ayyana Zaben Majalisar Tarayya a Matsayin Wanda Bai Kammala Ba, Ta Ba da Dalili

Kotu Ta Ayyana Zaben Majalisar Tarayya a Matsayin Wanda Bai Kammala Ba, Ta Ba da Dalili

  • Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci a mazabun Majalisar Tarayya da ke jihar Sokoto a yau Asabar
  • Kotun ta ayyana zaben mazabar Yabo/Shagari wanda bai kammala ba inda ta rusa zaben Honarabul Yusuf Yabo
  • Har ila yau, kotun ta tabbatar da nasarar Abdulsamad Dasuki a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Tambuwal/Kebbe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja da ayyana zaben mazabar Yabo/Shagari wanda bai kammala ba a jihar Sokoto.

Kotun ta ce hukuncin ya shafi rumfuna 26 inda ta rusa zaben Honarabul Yusuf Yabo, cewar Tribune.

Kotu ta raba gardama a shari'ar zaben Majalisar Tarayya a jihar Sokoto
Kotu ayyana zaben Majalisar Tarayya a jihar Sokoto wanda bai kammala ba. Hoto: Court of Appeal.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Sokoto?

Har ila yau, kotun ta tabbatar da nasarar Abdulsamad Dasuki a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Tambuwal/Kebbe a Majalisar Tarayya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta ruwaito cewa kotun ta tabbatar da nasarar Bashir Usman Gorau a matsayin zababben san Majalisar Tarayya a mazabar Gada/Goronyo da ke jihar Sokoto.

Dukkan mambobin Majalisar da aka tabbatar sun fito daga jami'yyar PDP bayan tabbatar da nasarar Saidu Bargaja da ke wakiltar mazabar Isa/Sabon Birni, cewar Latest News Nigeria.

Idan ba a manta ba, dan takarar jam'iyyar APC da aka ayyana wanda ya lashe zaben mazabar Isa/Sabon Birni, Abdulkadir Jelani ya rasu watanni biyu da su ka wuce.

Marigayin ya rasu ne a Abuja da yammacin wata ranar Talata bayan fama da jinya na tsawon lokaci, cewar Punch.

A martaninta, jam'iyyar PDP a jihar ta nuna jin dadinta kan wannan hukuncin kotun inda ta taya dukkan wadanda su ka samu nasara a shari'ar murna.

Kara karanta wannan

Nasara: Dakarun sojoji sun tarwatsa mafakar hatsabiban yan bindiga, sun kashe wasu a jihohin arewa 2

Kotu ta yi hukunci a shari'ar kakakin Majalisa

A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar kakakin Majalisar jihar Gombe wanda ke jam'iyyar APC, Abubakar Luggerewo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kotun har ila yau, ta yi watsi da karar Bashir Gaddafi na jam'iyyar PDP saboda rashin gamsassun hujjoji da zai ruguza zaben.

Wannan na zuwa ne bayan karamar kotu a baya ta rusa zaben kakakin Majalisar a mazabar Akko ta Tsakiya a jihar Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.