Kotun Koli: ‘Dan Majalisar NNPP Ya Sa Labule da Shugaba Tinubu a Kan Siyasar Kano

Kotun Koli: ‘Dan Majalisar NNPP Ya Sa Labule da Shugaba Tinubu a Kan Siyasar Kano

  • Abdulmumin Jibrin ya hadu da Mai girma shugaba Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock a ranar Juma'a
  • Jam’iyyar NNPP na neman yadda za ta tsira da kujerar gwamnan jihar Kano a shari’ar zaben 2023
  • ‘Yan siyasan sun tattauna a kan abin da ya shafi siyasar Kano yayin da ake jiran hukuncin kotun koli

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

FCT, Abuja - Hon. Abdulmumin Jibrin ya zauna da Bola Ahmed Tinubu, sun tattauna kuma a game da batun siyasar jihar Kano.

‘Dan majalisar wakilan tarayyan ya shaida haka a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a.

Tinubu-Kano
Abdulmumin Jibrin (NNPP) da Bola Tinubu Hoto: @AbdulAbmJ
Asali: Twitter

Hon. Abdulmumin Jibrin ya ce shi da Sanata Abubakar Sani Bello da Amb. Yusuf Tuggar su ka ziyarci fadar shugaban Najeriyan.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene aka tattauna da Tinubu?

Makasudin zuwan na su shi ne a tattauna harkokin huldatayyar Najeriya da kasashen waje.

Tsohon Jakadan Najeriya zuwa kasar Jamus, Hon. Yusuf Tuggar ne Bola Ahmed Tinubu ya zaba domin zama Ministan harkokin waje.

Tsohon gwamnan jihar Neja, Sanata Abubakar Sani Bello shi ne shugaban kwamitin harkokin kasar waje a zauren majalisar dattawa.

Jawabin Abdulmumin Jibrin (NNPP)

"Kafin yanzu a yau, ni da Sen. Abubakar Sani Bello da Amb. Yusuf Tuggar mun samu damar zama da Mai girma shugaban kasa a fadar gwamnati
Mun tattauna a kan tsare-tsaren hulda da kasashen ketare. Daga baya, ni da shugaban kasa mun tattauna a kan abin da ya shafi siyasar Kano da shugaban kasan."

- Abdulmumin Jibrin

NNPP za ta kai labari a kotun koli?

A halin yanzu jam’iyyar NNPP ta na neman samun nasara a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano da ta ke yi da APC mai mulki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da ke tsaka mai wuya ya samu natsuwa bayan 'yan majalisun Tarayya sun yi masa abu 1 tak

Kotun korafin zabe da ta daukaka kara sun ce Nasiru Gawuna ne zababben gwamna. Lauyoyin NNPP sun daukaka kara gaban kotun koli.

Kwankwaso ya zauna da manyan NNPP

A tsakiyar makon nan aka ji labari Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sa labule da wasu daga cikin kusoshi a tafiyar Kwankwasiyya.

Kawu Sumaila da wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya irinsu Abdulmumin Jibrin sun hadu da Madugun Kwankwasiyya a gidan na sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng