Abba vs Gawuna: Fitaccen Mawakin Siyasa Ya Yi Magana Kan Hukuncin Da Kotun Koli Za Ta Yanke
- Mawakin siyasar nan ɗan APC, Dauda Kahutu Rarara, ya yi magana kan zaman lafiya a Kano yayin da ake dakon hukuncin kotun ƙoli
- Fitaccen mawaƙin ya buƙaci ɗaukacin al'ummar jihar su zauna lafiya kana yaɓyaba da kokarin jami'an tsaro
- A watan Disamba da muke ciki ake tsammain kotun kolin Najeriya zata raba gardama a shari'ar zaɓen gwamnan Kano
Jihar Kano - Fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara ya yi kira da a zauna lafiya a jihar Kano.
Rarara tare da haɗin guiwar wasu fitattun jaruman Kannywood maza da mata sun roki jama'a kar su tada hankali yayin da ake dakon hukuncin kotun ƙoli kan zaben gwamnan jihar.
Kotun sauraron ƙararrakin zabe ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf, sannan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da wannan hukuncin, a yanzu kuma ana jiran hukuncin karshe na kotun koli.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta tsara yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnan Kano a wannan wata na Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Zamu taimaka wajen tabbatar da an zauna lafiya a Kano"
Da yake hira da ƴan jarida a Kano kan lamarin, Rarara ya ce a matsayinsu na mambobin APC masu bin doka da oda, zasu yi kokari a dukkan matakai domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Mawakin wanda ya yi ƙaurin suna a wakokin siyasa ya ƙara da cewa zasu ja hankalin magoya bayan APC a Kano da su zauna lafiya, babu tada yamutsi.
A cewar Rarara, zaman lafiya a jihar shine abu mafi muhimmanci don haka yana da matukar muhimmanci a kiyaye shi.
Ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci a yaba da kokarin jami’an tsaro tare da tallafa musu musamman dakarun ‘yan sanda, DSS da sauransu.
Tun da farko, tsohon shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Alhaji Isma’ila Afakallah, ya ce ɗabi'ar da mambobin APC suka nuna bayan an bayyana NNPP a matsayin wacce ta lashe zaɓe abun a yaba ne.
A cewarsa wannan hali da suka nuna na zaman lafiya ne ya sa APC ta samu nasara a kotun zaɓe da kuma kotun ɗaukaka ƙara.
Ministan Shugaba Tinubu ya canza jam'iyya a hukumance
A wani rahoton na daban Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce ya sake komawa jam'iyyar APC ne domin ya taimakawa Bola Ahmed Tinubu.
Adelabu ya bayyana cewa komawarsa jam'iyyar APC ba ta da alaƙa da burin zama magajin Gwamna Seyi Makinde a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng