Kano: Muhimman Abubuwa 2 Da Za Su Yanke Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Koli Tsakanin Abba da Gawuna

Kano: Muhimman Abubuwa 2 Da Za Su Yanke Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Koli Tsakanin Abba da Gawuna

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya garzaya kotun koli yana mai kalubalantar tsige shi da kotun ɗaukaka ƙara ta yi
  • Gwamnan na NNPP ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli ne biyo bayan hukuncin da ya kira na rashin adalci a ƙaramar kotu
  • Da yake hira da Legit Hausa, mai sharhi kan harkokin siyasa, Segun Akinleye, ya bayyana irin makircin da ake tafkawa a siyasar jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wani masani mai sharhi kan harkokin siyasa, Segun Akinleye, ya yi tsokaci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kano da ke gaban kotun ƙoli.

A cewarsa, abu ne mai matuƙar wahala a yanzu a iya hasashen wanda zai samu nasara a hukuncin da ake dako a kotun koli kan sahihin wanda ya lashe zaɓen Kano.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Fitaccen wawakin siyasa ya yi magana kan hukuncin da Kotun Koli za ta yanke

Gawuna da Gwamna Abba.
Zaben Kano: Muhimman Abu 2 da Zasu Yanke Wanda Zai Samu Nasara a Kotun Koli Hoto: Nasiru Gawuna, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Idan baku manta ba a watan Nuwamba, kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaɓe wanda ya tsige Gwamna Abba Yusuf na NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nan bada jimawa ba kotun ƙoli zata yanke hukunci

Sakamakon haka, kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta ayyana ɗan takarar APC, Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Saɓanin hukuncin da alƙalan kotun suka karanto, kwafin takardun hukuncin kotun ɗaukaka ƙara (CTC) ya nuna cewa kotun ta soke hukuncin kotun zaɓe kuma ta ci tarar APC N1m.

A halin yanzu kes ɗin ya kai ga kotun koli kuma kowane ɓangare na dakon hukuncin da zata yanke wanda shi ne na ƙarshe.

Yadda siyasar Kano take tsakanin APC da NNPP

Da yake tsokaci kan lamarin a wata hira da Legit Hausa, Akinleye ya ce zargi da tunanin maguɗin hukunci da son rai ba zai tabbatar da adalci ba.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Kotun ƙoli ta yanke hukunci kan makomar shugaban ƙungiyar ta'addanci IPOB

Ya kuma ambaci, "tasirin Wole Olanipekun" wanda Legit Hausa ta gano cewa Olanipekun (SAN) lauyan gwamnan Kano ne kuma lauyan NNPP.

Akinleye ya ce:

"Ruɗanin da ya biyo bayan kwafin takardun hukuncin kotun ɗaukaka ƙara naƙasu ne ga ɓangaren shari'a kuma ya jefa waswasi da ayar tambaya da ke buƙatar amsoshi."
"Akwai rikici mai zafi a Kano, shugaban APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan da ya sauka, Abdullahi Ganduje zai yi bakin kokarinsa ya ga APC ta ci gaba da mulki."
"Shi kuma gwamna mai ci ya rushe gine-gine masu yawa waɗanda Gwamnatin Ganduje ta gina, saboda haka adawar da ke tsakaninsu da kai da kai ce."
'Tasirin Wole Olanipekun wani abu ne da ya kamata a zuba ma ido. Bana tunanin zamu kara shaida irin hukuncin Gwamna Uzodinma, lokacin da ya zama gwamna bayan ya zo na huɗu."

Jam'iyyar APC Ta Fara Shin Tsige Gwamna

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ta fara duba yiwuwar tsige Gwamna Fubara na jihar Ribas kan yi wa doka hawan kawara.

Shugaban kwamitin riƙon APC na jihar, Okocha, ya ce gwamnan ya fara wuce gona da iri wajen karya dokar kwansutushin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel