‘Yar Majalisa Ta Fadi Hakikanin Abin da Ya Hada Wike da Gwamna Fubara Fada a Jihar Ribas

‘Yar Majalisa Ta Fadi Hakikanin Abin da Ya Hada Wike da Gwamna Fubara Fada a Jihar Ribas

  • Akwai ‘yan majalisar wakilan da ba su goyon bayan Nyesom Wike a rigimarsa da gwamnan jihar Ribas
  • ‘Yan majalisar sun zargi Ministan Abuja da kokarin juya Gwamna Similanayi Fubara duk da ya bar ofis
  • Boma Goodhead da Awaji-Inombek Abiante suna so Bola Ahmed Tinubu ya takawa Ministan Abuja burki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya daga jihar Ribas sun yi kira ga Bola Ahmed Tinubu da ya ja kunnen Nyesom Wike.

Labarin da aka samu daga Vanguard ya ce wasu masu wakiltar Ribas a majalisar tarayya sun yi magana a kan rikicin siyasar jihar.

Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike
Nyesom Wike da Simi Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Hakan yana zuwa ne bayan kwamishinoni da-dama sun ajiye aikinsu a dalilin sabanin Nyesom Wike da Gwamna Simi Fubara.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ana zargin Shugaba Tinubu da rura wutar rikici a jihar PDP, bayani sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan majalisan da ke goyon bayan Fubara

Awaji-Inombek Abiante ya jinjinawa Mai girma Simi Fubara a kan matakin da ya dauka domin gyaran ginin majalisar dokokin Ribas.

Haka kuma ‘yan majalisar tarayyan biyu sun yi tattaki domin nuna su na goyon bayan ayyukan Siminalayi Fubara a jihar ta Ribas.

Boma Goodhead mai wakiltar Toru/Akuku Toru a majalisa da Hon Awaji-Inombek Abiante na Andoni/Opobo/Nkoro ba su tare da Wike.

Wadannan ‘yan majalisa biyu sun yi zanga-zangar lumana suna cewa Wike yana rigima da Fubara ne saboda ya ki yarda ya juya shi.

Abin da ya hada Wike da Fubara fada

‘Yar siyasar ta ce gwamna Fubara ya zabi ya yi wa al’ummar Ribas aiki a maimakon ya bari tsohon gwamnan ya cigaba da mulkarsu.

Hon. Goodhead ta ce Wike bai neman zaman lafiya a Ribas, saboda haka ya kamata shugaban kasa Bola Tinubu ya ja kunnen ministan.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya maida zazzafan martani yayin da ake shirin tsige shi daga kan mulki

Idan ministan harkokin Abuja ya sake zuwa Ribas, ‘yar majalisar ta ce ba za su zura ido a tada rikici ba. The Nation ta kawo rahoton nan.

Wike ya rusa majalisar Jihar Ribas

A makon nan aka ji labari gwamnatin jihar Ribas ta ruguza majalisar da sunan ginin yana da matsala, lamarin da ya jawo surutu a kasa.

Ana zargin sauya-shekar 'yan majalisa zuwa APC ne ya jawo aka yi hakan. 'Yan majalisa 27 cikin magoya bayan Wike sun koma PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng