Wike vs Fubara: Karin Kwamishinoni Biyu Sun Yi Murabus a Jihar Rivers, Adadin Ya Kai 6 Yanzu

Wike vs Fubara: Karin Kwamishinoni Biyu Sun Yi Murabus a Jihar Rivers, Adadin Ya Kai 6 Yanzu

  • Rahotan da Legit Hausa ta samu yanzu na nuni da cewa wasu kwamishononi biyu sun yi murabus daga gwamnatin jihar Rivers
  • Ajiye aikin kwamishinonin biyu a safiyar yau na nuni da cewa Gwamna Fubara ya rasa kwamishinoni shida daga Alhamis zuwa Juma'a
  • Rikicin siyasar jihar Rivers na ci gaba da tsamari tsakanin Nyesom Wike da Gwamna Fubara, lamarin da ya shafi gudanar da ayyuka a Rivers

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Rivers - Guguwar ajiye mukamai daga mukarraban gwamnatin jihar Rivers na ci gaba da kadawa, inda a ranar Juma'a aka samu karin kwamishinoni biyu da suka ajiye aiki.

A jiya Alhamis ne kwamishinoni hudu da ke goyon bayan ministan Abuja Nyesom wike suka yi murabus daga gwamnatin Fubara.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗau zafi, ya umarci wasu kwamishinoni su yi murabus nan take

Karin kwamishinoni biyu sun yi murabus a jihar Rivers
Rikicin Nyesom Wike da Gwamna Fubara na kara tsamari, an samu karin kwamishinoni biyu da suka yi murabus a ranar Juma'a. Hoto: @GovWike, @SimFubaraKSC
Asali: Facebook

Kwamishinan ilimi na jihar Rivers, Farfesa Prince Chinedu da kwamishiniyar gidaje, Gift Worlu (PhD) su ne sabbin kwamishinonin da suka yi murabus a ranar Juma'a, Channels TV ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba, antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar, Farfesa Zacchaeus Adangor ne ya fara ajiye aikinsa a cikin kwamishinonin, Rahoton Channelstv.

Kwamishinan ayyuka George-Kelly Alabo, wanda ya taba rike irin mukamin a zamanin Nyesom Wike, da kwamishiniyar jin dadi da bunkasa rayuwar jama'a, Inime Aguma, da kwamishinan kudi Isaac Kamalu sun ajiye aikin su a jiya Alhamis.

Gwamna Fubara ya fadi dalilin rushe ginin majalisar dokokin jihar Rivers

A wani labarin kuma, Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta rushe gininin majalisar dokokin jihar ne don gina sabuwa biyo bayan gobara da ta lalata ta.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tabbatar da barin Ciyamomi 21 da Kansiloli 239 ofisoshinsu, ya fadi dalili

Vanguard ta ruwaito sanarwar na cewa Fubara ya amince 'yan majalisun jihar su yi amfani da wani sashe da ke cikin fadar gwamnatin jihar don gudanar da zaman su.

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta kawo maku rahoton yadda gobara ta tashi a wani bangare na zauren majalisar dokokin jihar, lamarin da ya biyo da fashewar wani abu.

Gwamna Fubara ya kira masana kan harkar gini, wadanda suka gudanar da bincike kan karkon ginin majalisar, a karshe kuma suka bashi shawarar rushe ginin tare da gina sabuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.