Wike vs Fubara: Cikakkun Jerin Kwamishinonin da Suka Yi Murabus Zuwa Yanzu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Rikicin siyasar jihar Ribas ya dauki sabon salo yayin da kwamishinonin Gwamna Siminalayi Fubara suka fara yasar da gwamnan sakamakon kin yin sulhu da magabacinsa kuma ubangidansa, Nyesom Wike.
Akalla kwamishinoni takwas cikin 18 ne suka mika wasikunsu na barin aiki zuwa safiyar Juma'a, 5 ga watan Disamba.
Kwamishinoni sun fara ajiye aiki awanni 24 bayan gwamnan ya rusa zauren majalisar dokokin jihar Ribas da kuma gabatar da kasafin kudinsa na sama da naira biliyan 800 ga yan majalisa hudu masu biyayya gare shi a gidan gwamnati.
A safiyar ranar Alhamis, gwamnan ya sanya hannu a kasafin kudi, kuma kafin karshen ranar akalla kwamishinoni shida suka yi watsi da Fubara. Ga jerin kwamishinonin a kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Cif Dr. Jacobson Nbina JP
Nbina ya kasance kwamishinan sufuri wanda ya mika takardar murabus din sa a ranar Juma’a.
Yayin da yake godewa gwamnan, Nbina ya bayyana dalili na kashin kai da matsalolin iyaye a matsayin dalilin murabus dinsa.
2. Gift Worlu
Worlu shine kwamishinan gidaje, wanda ya mika wasikar ajiye aiki ga Gwamna Fubara.
Yayin da yake alkawarin ci gaba da ba da goyon baya ga walwala da ci gaban al’ummar jihar, Worlu ya kuma bayyana dalili na kashin kai da ke bukatar kulawarsa cikin gaggawa.
3. Farfesa Zacchaeus Adangor
Adangor shine atoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar. Shine kwamishina na farko da ya mika takardar barin aiki ga Gwamna Fubara.
Farfesan wanda ya kuma yi aiki a matsayin atoni janar karkashin gwamnatin Wike, ya ce ya ajiye aikin ne saboda dalili nasa na kansa.
4. Dr Des George-Kelly
George-Kelly, wanda shi ne kwamishinan ayyuka a karkashin Gwamna Fubara, shi ma ya mika takardar murabus dinsa a ranar Alhamis.
Kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto, tsohon kwamishinan ya bayyana cewa zuciyarsa ba zai bar shi ya ci gaba da aiki da gwamnan ba.
5. Emeka Woke
Woke shi ne kwamishinan ayyuka na musamman kuma yana daya daga cikin kwamishinoni na farko da suka mika takardar murabus dinsu.
Ya kasance shugaban ma'aikatan Wike na tsawon shekaru takwas a jere.
6. Misis Inime Aguma
An nada Aguma a matsayin kwamishinar jin dadi da walwala amma kuma ta mika takardar murabus dinta bayan rusa majalisar dokokin jihar.
A cikin wasikar murabus din ta, ta bayyana cewa tana da sauran ayyuka.
7. Isaac Kamalu
Kamalu, kwamishinan kudi na jihar shi ma ya bi sahun masu yin murabus wanda ya girgiza gwamnatin gwamna Fubara a ranar Alhamis.
Da yake mika godiyarsa ga gwamnan, bai bayar da wani dalili na yin murabus ba yayin da ya bayyana cewa zai fara aiki nan take.
8. Farfesa Chinedu Mmom
Mmom, kwamishinan ilimi na jihar, bai bayyana dalilinsa na yin murabus ba, sai dai ya yiwa gwamnan fatan alheri. Ya ce:
"Ina so in nuna godiya ta ga damar da aka ba ni na yin aiki a cikin gwamnatin ka tare da yi maka fatan alheri yayin da kake ci gaba da gudanar da mulkin jihar."
APC na zawarci ministan Abuja
A wani labarin, mun ji cewa APC mai rike da mulkin kasa ta kara kaimi wajen ganin ta dauke Nyesom Wike daga jam’iyyar hamayya watau PDP.
Labari ya zo daga Daily Trust cewa shugabannin jam’iyyar APC sun yi wa Nyesom Wike alkawarin shugabanci idan ya bar PDP.
Asali: Legit.ng