Tinubu: Mutum 2 da Za Su Taimakawa Gwamnatinmu Wajen Samun Nasara a Najeriya

Tinubu: Mutum 2 da Za Su Taimakawa Gwamnatinmu Wajen Samun Nasara a Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya halarci bikin da aka shirya domin taya Godswill Akpabio murnar cika shekara 61 a duniya
  • Shugaban kasar ya jinjinawa shugaban majalisar dattawa, ya ce ya yi abin kwarai tun yana mulkin jihar Akwa Ibom
  • Mai girma Tinubu ya ce zaman Rt. Hon. Tajudeen Abbas shugaban majalisar wakilai ya taimakawa gwamnatinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya ce yunkurin gwamnatinsa na kawo sauyi a Najeriya ya fara haifar da ‘da mai ido tun kafin ayi nisa.

A rahoton This Day na ranar Alhamis, shugaban kasan ya ce a dalilin Godswill Akpabio da Rt. Hon. Tajudeen Abbas yake cin nasara.

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

Tinubu
Bola Tinubu a bikin Godswill Akpabio Hoto: @Dolusegun16
Asali: Twitter

Godswill Akpabio ya cika 61

Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya ce shugabannin majalisar tarayyan suna taka rawar gani wajen ganin an magance matsalolin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Najeriyan ya yi jawabi ne wajen bikin da aka shiryawa Godswill Akpabio domin taya sa murnar cika shekara 61 da haihuwa.

"Samun Akpabio a shugaban majalisar dattawa da Abbas a matsayin shugaban majalisar wakilan tarayya a bangare na sun isa su taimaka mani wajen yin nasara, kuma za mu yi nasara."

- Bola Tinubu

An rahoto Bola Tinubu yana mai cewa shugaban majalisa watau Akpabio yana da hali na gari.

Shugaba Tinubu ya yabawa Godswill Akpabio

Tinubu ya ce Akpabio ya fara ne daga kwamishina har ya zama gwamnan Akwa Ibom, a mulkinsa na shekaru takwas ya yi koyi da tsarin Legas.

Ko da Tinubu yake gwamna tsakanin 1999-2007, Akpabio yana kwamshina, shugaban kasar yace bai san zai zama gwamnan Akwa Ibom ba.

Kara karanta wannan

Yanzu: Tinubu ya yi kokarin sulhu tsakanin Wike da Fubara, APC ta yi karin haske

'Yan majalisa ko 'yan amshin shatan Tinubu?

Leadership ta ce tsohon shugaban NBA, Dr Olisa Agbakoba (SAN) ya ce hanyar samun zaman lafiya a kasar shi ne majalisa ta zauna da Sarakuna.

Lauyan ya ce ana watsi da sarakuna a majalisar tarayya, wanda shugaban kasa ya ce gashin kan su su ke ciki ba ‘yan amshin shatansa ba ne.

Kasafin kudin Tinubu a Majalisa

Ku na da labari akalla Ministoci uku su ka ce kasafin kudin shekarar 2024 da aka yi ba zai je ko ina ba, su ka bukaci majalisa ta kara masu kudi.

Badaru Abubakar ya roki a kara masa kudi saboda tashin farashin dizil da man fetur bayan Bola Tinubu ya gabatar da kundin ga 'yan majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng