Babbar matsala ga gwamna yayin da ƴan majalisa 26 suka yi zama na musamman, bayanai sun fito

Babbar matsala ga gwamna yayin da ƴan majalisa 26 suka yi zama na musamman, bayanai sun fito

  • Mambobi 26 na majalisar dokokin jihar Ribas sun yi zama a ɗakin taro na rukunin gidajen ƴan majalisu ranar Alhamis
  • Wannan zama na zuwa ne kwana ɗaya bayan Gwamna Fubara ya sa an rushe zauren majalisar dokokin jihar
  • Gwamnan wanda ke takun saka da ministan Abuja, Nyesom Wike, ya rattaba hannu a kasafin kuɗin 2024 na N800bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mambobi 26 na majalisar dokokin jihar Ribas sun yi zama ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, 2023.

Yan majalisun waɗanda suka sauya sheka zuwa APC kwanan nan, sun yi zaman ne a ɗakin taron da ke rukunin gidajen yan majalisa a Fatakwal.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kwamishinoni huɗu sun yi murabus daga muƙamansu a jihar PDP, sun faɗi dalili

Gwamna Fubara da Ministan Abuja.
Yanzu: Babbar matsala ga gwamna yayin da ƴan majalisa 26 suka yi zama na musamman, bayanai sun fito Hoto: Sim Fubara, Nyesom Wike
Asali: Twitter

Mambobin majalisar sun gudanar da wannan zama ne sa'o'i 24 bayan Gwamna Siminialayi Fubara ya rushe zauren majalisar dokokin jihar Ribas, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara ya sa hannu a kasafin kuɗin 2024

Wannan zama na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ya rattaba hannu kan kudirin kasafin kuɗin shekarar 2024 wanda zai laƙume N800bn.

Fubara ya sanya hannu kan kasafin kudin ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, 2023 a gidan gwamnatin jihar Ribas da ke Fatakawal, rahoton PM News.

Hakan ya faru ne kwana ɗaya bayan gwamnan ya miƙa kunshin kasafin ga mambobin majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Edison Ehie, mai goyon bayansa.

Da yake jawabi a wurin, Gwamna Fubara ya ce gwamnatinsa za ta maida hankalin wajen gina muhimman tituna da zasu haɗa kauyuka a faɗin kananan hukumomin Ribas.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bada mamaki kwana daya bayan miƙa kasafin kuɗin 2024 ga majalisa

A kalamansa ya ce:

"Wannan kasafi ya nuna ƙarara cewa muna da shiri mai kyau ga jihar mu. Ɗaya daga cikin dalilin da yasa kasafin ya kai N800bn shi ne mun yi niyyar cika aƙalla buƙatar jiharmu guda ɗaya."
"Da taimakon Allah zamu fara aiki ba kama hannun yaro, zuwa shekara mai zuwa zamu fara da buɗe aikin titin Trans-Kalabari sashi na 2."

Kwamishina ya yi murabus a jihar Ribas

A wani rahoton na daban Antoni janar na jihar Ribas kuma kwamishinan shari'a, Zacchaeus Adangor, ya yi murabus daga mukaminsa.

Adangor ya aika takardar murabus dinsa mai kwanan wata 14 ga watan Disamba, 2023 zuwa ga Gwamna Siminalayi Fubara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262