Mataimakin Gwamna Ya Zama Mukaddashin Gwamna a Jihar APC
- Majalisar dokokin jihar Ondo ta ayyana mataimakin gwamna Rotimi Akeredolu, Lucky Aiyedatiwa a matsayin mukaddashin gwamnan jihar
- Kakakin majalisar dokokin jihar, Olamide Oladiji, ya ce daukar matakin ya zama dole bayan samun takardar miƙa mulki daga gwamnan da ke fama da rashin lafiya
- Olamide Oladiji ya bayyana cewa zai sanar da magatakardar majalisar tsarin doka na gaba da za a bi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Olamide Oladiji, kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, ya ce a yanzu mataimakin gwamna Lucky Aiyedatiwa ne zai zama muƙaddashin gwamnan jihar.
Sanarwar ta biyo bayan samun wasiƙar Gwamna Rotimi Akeredolu kan miƙa mulki ga Aiyedatiwa, cewar rahoton jaridar The Nation.
A cewar Oladiji, akwai buƙatar a bi tsarin mulki, kuma zai buƙaci magatakardar majalisar ya sanar da sakataren gwamnatin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar ya ce ƴan majalisar na sane da ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu kuma sun amince da wasiƙar Gwamna Akeredolu.
Ya ƙara da cewa majalisar ba za ta zauna kan lamarin ba, don haka za a fitar da sanarwa bayan an kammala miƙa mulki.
Meyasa aka ayyana Aiyedatiwa muƙaddashin gwamna?
Dangane da hakan, kakakin ya ce Aiyedatiwa zai ci gaba da riƙe muƙamin gwamnan jihar har sai an samu wata sabuwar sanarwa.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
"Bayan shawarar da likitan ya bayar game da buƙatar sake zuwa duba lafiyarsa bayan ya samu sauƙi, gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Odunayo Akeredolu, SAN, CON, ya miƙa wasiƙan kan tafiya hutun jinya ga majalisar dokokin jiha."
Shugaban majalisar ya bayyana cewa matakin na Gwamna Akeredolu ya yi daidai da sashe na 190 na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima.
Rashin lafiyar Akeredolu ta haifar da rikicin siyasa a jihar yayin da wasu ƴan majalisar dokokin jihar ke yunƙurin tsige mataimakin gwamnan bayan kiran da aka yi na ayyana shi a matsayin muƙaddashin gwamna.
Sai dai, shiga tsakanin da Shugaba Bola Tinubu ya yi ya kawo daidaituwar al'amura yayin da dukkan bangarorin suka amince cigaba su zauna tare.
Tinubu Ya Aike da Umarni Ga Majalisar Ondo
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci majalisar dokokin jihar Ondo, da ta miƙa mulki ga mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a taron da ya kira domin magance rikicin shugabanci a jihar Ondo.
Asali: Legit.ng