Rikicin Rivers: Babban Lauya Ya Bayyana Matsayar Kujerun Yan Majalisa 27 na PDP da Suka Koma APC

Rikicin Rivers: Babban Lauya Ya Bayyana Matsayar Kujerun Yan Majalisa 27 na PDP da Suka Koma APC

  • Wani lauya Kalu Kalu Agu ya bayyana cewa ƴan majalisar dokokin jihar Rivers 27 da suka fice daga PDP zuwa APC sun rasa kujerunsu a majalisar
  • Kalu ya bayyana cewa wanda aka zaɓa na iya sauya sheka daga jam’iyyarsa zuwa wata a lokacin wa’adinsa idan har aka samu rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar
  • Kalu ya bayyana cewa jam’iyyar PDP tana gudanar da al’amuranta ba tare da wani rikicin shugabanci ba a faɗin ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - Wani lauya, Kalu Kalu ya ce ƴan majalisar dokokin jihar Rivers 27 da suka fice daga jam’iyyar PDP kwanan nan a jihar Rivers sun rasa kujerunsu a majalisar.

Idan ba a manta ba dai a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba, ƴan majalisar jihar Rivers 27 sun fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Rivers: An ba INEC sabon wa'adi kan yan majalisar PDP da suka koma APC

Lauya ya bayyana makomar yan majalisar Rivers
Yan majalisar masu biyayya ga Wike sun koma APC Hoto: @Topboychriss, @GovWike
Asali: Twitter

"Kujerun ƴan majalisar Rivers 27 sun riga sun zama babu kowa.” - Lauya

Kalu, a wata hira da yayi da kafar yada labarai ta Arise News a ranar Talata, 12 ga watan Disamba, ya bayyana cewa doka ta bayyana cewa wanda aka zaɓa na iya sauya sheka daga jam’iyyarsa zuwa wata a lokacin wa’adin mulkinsa idan har ana rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa:

"Ƴan majalisu 27 da abin ya shafa, kujerunsu sun riga sun zama babu kowa, bisa tanadin kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 kamar yadda ya tanada."
"Da zarar kun sauya sheƙa daga jam'iyyar da kuka ci zabe, zuwa wata jam'iyyar kafin ƙarewar wa'adin majalisar da aka zaɓe ku, to kai tsaye za ku rasa wannan kujera."

An Ba INEC Wa'adi Kan Ƴan Majalisar Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta samu wa'adi kan ƴan majalisar dokokin jihar Rivers 27 na jam'iyyar PDP da suka koma jam'iyyar APC.

Ƙungiyar National Democratic Congress (NDC) ta ba INEC wa'adin kwana 14 da ta gudanar da zaɓe domin maye gurbin ƴan majalisar da suka sauya sheƙa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng