Rivers: An Ba INEC Sabon Wa'adi Kan Yan Majalisar PDP da Suka Sauya Sheka Zuwa APC
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta samu sabon wa'adi ƙam ƴan majalisar dokokin jihar Rivers da suka koma APC
- Ƙungiyar National Democratic Congress (NDC) ta ba INEC wa'adin kwana 14 domin gudanar da zaɓen maye gurbinsu
- A cewar ƙungiyar sauya sheƙar da suka yi daga PDP zuwa APC ya sanya sun rasa kujerunsu a tsarin doka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar National Democratic Congress (NDC) ta bayar da wa’adin kwanaki 14 ga hukumar INEC da ta shirya zaɓen cike gurbi na mazabu 27 da ba kowa a majalisar dokokin jihar Rivers.
Wannan buƙata ta zo ne a matsayin martani ga ficewar ƴan majalisa 27 daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata, 12 ga watan Disamba, Daniel Okwa, shugaban ƙungiyar, ya bayyana damuwarsa game da tasirin abubuwan da suka faru a Rivers a baya-bayan nan ga dimokuradiyya a ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan majalisar sun saɓa doka
Okwa ya jaddada cewa, a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, mambobi 27 da suka sauya sheka sun bar kujerunsu a majalisar dokokin jihar, lamarin da zai sa a yi sabon zaɓe.
Da yake tsokaci daga kundin tsarin mulki, Okwa ya bayyana cewa:
"Ɗan majalisa zai bar kujerarsa a majalisa, idan kasancewarsa wanda jam’iyyar siyasa ce ta ɗauki nauyin zaɓensa a majalisar, ya zama ɗan wata jam’iyyar siyasa kafin karewar wa’adin majalisar."
"Ƴan majalisar guda 27 dole ne kawai su bi matsayin doka ta hanyar ficewa daga majalisar dokokin jihar Rivers bayan da suka karya sashe na 109 (g) na kundin tsarin mulkin da ya kawo su."
"A ƙarƙashin dokar, wadannan ƴan majalisar sun daina zama wakilan jama’a, kuma dole ne a bayyana ofisoshinsu a matsayin wadanda ba kowa ba."
Ƙungiyar ta yi barazanar zanga-zanga
Kungiyar ta yi gargadi, inda ta jaddada cewa idan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa bin ka’idojin doka, ƴan ƙasa za su ɗauki mataki kan hukumar zabe.
Kungiyar ta ce:
"Muna kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya fito fili ya yi Allah-wadai da aika-aikar da ake yunƙurin yi da sunan jam’iyyar siyasar da yake shugabanta ta APC."
"Ya kamata shugaban ƙasa ya faɗa wa Wike da tsaffin ƴan majalisa a fili cewa ba za a iya alakanta shi ko ganin yana karfafa wannan yi wa doka karan tsayen ba."
An Ba Tinubu Shawara Kan Rikicin Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Ijaw Congress ta shawarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan rikicin siyasar jihar Rivers.
Ƙungiyar ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya shiga tsakani a rikicin wanda ke faruwa tsakanin tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara.
Asali: Legit.ng