Tinubu Ya Fusata, Ya Sake Saka Baki a Rikici Tsakanin Gwamnan APC da Mataimakinsa, Ya Dauki Mataki

Tinubu Ya Fusata, Ya Sake Saka Baki a Rikici Tsakanin Gwamnan APC da Mataimakinsa, Ya Dauki Mataki

  • A karshe, Tinubu ya sake shiga lamarin rikicin siyasa a jihar Ondo da niyyar kawo karshensa
  • A jiya Litinin, Tinubu ya sake gayyatar mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa da kakakin Majalisar, Olamide Oladiji
  • Wannan shi ne karo na biyu da shugaban ke shiga lamarin amma wannan shi zai zama na karshe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Shugaba Tinubu ya sake shiga lamarin rikicin siyasa ta ke kara kamari a jihar Ondo.

A jiya Litinin 11 ga watan Disamba, Tinubu ya sake gayyatar mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa da kakakin Majalisar, Olamide Oladiji.

Tinubu ya sake saka baki a rikicin siyasar jihar Ondo
Tinubu ya fusata kan rikicin siyasar jihar Ondo. Hoto: Lucky Aiyedatiwa, Bola Tinubu, Rotimi Akeredolu.
Asali: Facebook

Su wa ye Tinubu ya gayyata a taron rikicin siyasar?

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 3 da suka faru gabanin yan Majalisa 27 su sauya sheka daga PDP zuwa APC

Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya shiga tsakani a rikicin siyasa da ta addabi jihar saboda yadda Gwamna Rotimi Akeredolu ya zama a jihar. Rotimi Akeredolu ya gagara zama a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa Sakataren Gwamnatin jihar, Oladunni Odu da shugabann jami'yyar APC a jihar, Ade Adetimehin su ma sun samu halartar ganawar.

Wata majiya ta tabbatar da cewa Tinubu ya yi hakan ne don kawo karshen rikicin siyasa a jihar wacce ta ki ci ta ki cinyewa, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Wace damuwa Tinubu ya nuna kan rikicin?

Majiyar ta ce:

"Da gaske ne Tinubu ya sake kiran jagororin jihar don sake zama kan rikicin siyasar ta karshe.
"A kwanakin baya shugaban ya saka baki da zimmar kawo karshen rikicin amma sai su ka koma gida su ka ci gaba da ruruta rikicin.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki yayin da wani mutum ya kashe da birne mahaifiyarsa da kanwarsa a karamin rami

"Tabbas Tinubu ya damu a wannan lokaci kuma ina tunanin zai bar kundin tsarin mulki ya yi aiki ne ganin yadda zabe ke karatowa a jihar."

Tinubu ya sake martani kan harin bam a Kaduna

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin ci gaba da taimakawa wadanda iftila'in harin bam ya rutsa da su a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.

Tinubu ya ce tabbas sun mutu su na maimaita kalmar shahada kuma sun mutu shahidai yayin da harin bam na sojoji ya hallaka su a kauyen Tudun Biri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.