PDP: Duk Wani ‘Dan Majalisar Dokokin da ya Koma APC a Ribas Ya Rasa Kujerarsa
- Jam’iyyar PDP ta ce dole hukumar INEC ta sake zabe tun da wasu 'yan majalisan Ribas sun dawo APC
- Sakataren yada labaran PDP ya ce ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas sun rasa kujerun da su ke kai
- Jawabin Hon. Debo Ologunagba ya nuna kundin tsarin mulki ya ce sauya-sheka na nufin rasa kujera
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Jam’iyyar PDP ta fitar da jawabi na musamman a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba 2023, a kan rikicin siyasar jihar Ribas.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba a jawabin da aka fitar a X ya bukaci a shirya sabon zabe a Ribas.
PDP ta ce INEC ta shirya wani zabe a Ribas
Hon. Debo Ologunagba ya ce dokar kasa ta tabbatar da duk ‘dan majalisar dokokin da ya bar PDP zuwa APC a Ribas ya rasa kujerarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin jam’iyyar hamayyar ya bukaci hukumar INEC ta gudanar da sabon zabe a mazabun da wadannan ‘yan majalisa su ka fito.
Abin da dokar kasa ta ce a ka batun Ribas
Ologunagba yake cewa sashe na 109 (1) (g) na kundin tsarin mulkin 1999 ya ce ‘dan majalisa zai rasa kujerarsa idan ya sauya-sheka.
Muddin ‘dan majalisa ya bar jam’iyyarsa kafin wa’adinsa ya kare, PDP ta ce doka ta wajabta masa barin kan matsayin da aka zabe shi.
Jawabin Kakakin Jam'iyyar PDP
"Saboda wannan dalili na tsarin mulki da kuma yadda kotun koli ta fassara shi a zahiri, ‘yan majalisa 27 da su ka sauya-sheka a majalisar dokokin jihar Ribas sun yi asarar kujerarsu, sun rasa duk wata alfarma ta majalisar dokokin Ribas.
Saboda haka jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban majalisar dokokin jihar Ribas ya bi tsarin mulki ta hanyar ayyana cewa sun rasa kujerarsu.
A dalilin wannan gibi da aka samu a mazabu 27 na jihar Ribas, PDP ta nemi INEC ta shirya sabon zabe a lokacin da dokar tarayyar Najeriya ta shekarar 1999 ta yi tanadi domin a maye gurabensu."
- Sakataren yada labaran PDP, Hon. Debo Ologunagba
A karshen jawabinsa, kakakin na PDP ya nemi tsofaffin ‘yan majalisan su daina ikirarin su na kan mukamansu, su bar shiga rigar wasu.
Meya jawo 'yan Majalisan Ribas shiga APC?
Anabs Sara-Igbe ya fito yana cewa shirin tsige Gwamnan Ribas ne ya yi sanadiyyar da ‘yan majalisar dokoki suka sauya sheka zuwa APC.
A cewar wani ‘dan majalisar dokoki, za su lashe zabe ko a APC kuma ya ce Nyesom Wike bai bar PDP ya shigo jam’iyyar APC mai mulki ba.
Asali: Legit.ng