'Muhimman Abubuwa 3 Da Suka Faru Gabanin Yan Majalisa 27 Su Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC'

'Muhimman Abubuwa 3 Da Suka Faru Gabanin Yan Majalisa 27 Su Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC'

  • Jigon APC a Oyo, Akin Akinwale, ya jero wasu batutuwa uku da suka faru gabanin mambobi 27 na majalisar dokokin Ribas su sauya sheƙa
  • A cewarsa ƴan majalisar waɗanda aka gani a bidiyo suna rera waƙar Shugaba Tinubu sun koma APC kwana kaɗan bayan Wike ya yi irin haka
  • Nyesom Wike, ministan Abuja kuma tsohon gwamnan Ribas na takun saka da Gwamna Fubara kuma ƴan majalsar suna tare da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Wani jigon APC daga jihar Oyo, Akin Akinwale, ya bayyana wasu abubuwa aƙalla uku da suka auku gabanin sauya sheƙar 'yan majalisar dokokin jihar Ribas.

A cewarsa, "siyasa ce silar shugabanci," yana mai cewa har yanzun rikicin siyasar da ke tsakanin Gwamna Similanayi Fubara da Nyesom Wike, ministan Abuja bai ƙare ba.

Kara karanta wannan

An aike da sako ga Tinubu yayin da yan majalisa masu biyayya ga Wike suka shirya tsige Fubara

Gwamna Fubara da Wike.
Rikicin Rivers: Jigon APC ya lissafo abinda ya faru kafin yan majalisa 27 su fice PDP Hoto: Sim Fubara, Nyesom Wike
Asali: Twitter

Idan baku manta ba, yan majalisa 27 daga cikin 32 na majalisar dokokin jihar Ribas sun tattara kayansu daga PDP zuwa APC a kwanan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rigima ta mamaye siyasar Ribas

Tun da farko, yan majalisar sun aika sakon sanarwa ga Gwamna Fubara cewa sun fara shirin tsige shi daga mulki, lamarin da Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya shiga tsakani.

Bayan wannan lokaci, Gwamna Fubara ya lashi takobin kare kujerarsa kuma an ga yadda ya naɗa na shi kakakin majalisar dokokin jihar.

A nasa bangaren, Wike ya soki Gwamna Fubara cewa yana kokarin rusa tsarin siyasar jihar watanni shida bayan ya taimaka masa ya ci zaɓe. A cewarsa Fubara ba mai biyayya bane.

Kwatsam da safiyar ranar Litinin, 11 ga watan Disamba, 2023, aka ga ƴan majalisa 27 a wani faifan bidiyo suna rera waƙar Tinubu bayan sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame fadar babban sarki, sun kwato makamai

Jigon APC ya maida martani

Da yake martani kan lamarin a shafinsa na manhajar X, Mista Akinwole ya jero wasu abubuwa da suka auku gabanin sauya sheƙar 'yan majalisar, ya ce Wike ne a sama.

Ya wallafa a shafinsa cewa:

"APC ta kori shugabanninta na jihar Ribas kuma ta naɗa kwamitin riƙon kwarya wanda Wike ke da tasiri a ciki. Kwanaki kaɗan bayan haka shugaban PDP na jihar ya yi murabus ya karɓi muƙami a gwamnatin APC."
"Kwanaki kalilan bayan haka aka ga Minista Wike na tiƙa rawar Akwaba a ofishin shugaban ma'aikata, kwatsam kuma sai mambobi 27 daga cikin 32 na majalisa masu goyon bayansa suka koma APC."
"Amma Sadiq Tade ya zo nan yana yabon Fubara da wasu bidiyon TikTok yana roƙon FG ta tsoma baki a rikicin, ya manta siyasa ce ke kawo shugabanci."

Gwamna Fubara ya shiga ganawar sirri

A wani rahoton na daban Yayin da Gwamna Fubara na jihar Rivers ke cikin tashin hankali na yiyuwar tsige shi, ya shiga ganawar sirri da majalisar zartarwa a jihar.

Kwanan nan ne 'yan majalisun jihar 27 daga cikin 32 su ka sauya sheka zuwa APC daga PDP yayin da ke tsaka da rikicin siyasa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262