Wike v Fubara: Asalin Dalilin ‘Yan Majalisan Ribas Na Dawowa APC Inji Jagororin Jam’iyya
- A matsayinsa na jigo a jam’iyyar APC a Ribas, Anabs Sara-Igbe ya yi magana a kan siyasar da ake bugawa
- ‘Dan siyasar ya ce ba komai ya jawo ‘yan majalisa akalla 27 su ka fice daga PDP zuwa APC sai tsige gwamna
- Anabs Sara-Igbe ya zargi Nyesom Wike da kin ajiye kayan yaki duk da an yi masu sulhu a fadar shugaban kasa
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Rivers - Anabs Sara-Igbe jagora ne daga cikin jagororin jam’iyyar APC a Ribas, ya yi magana game da siyasar da ake bugawa a jihar.
Da aka yi hira da shi a Channels, Anabs Sara-Igbe ya ce sauya-shekar ‘yan majalisa 27 daga PDP zuwa APC shirin tunbuke gwamna ne.
Gwamna Siminialayi Fubara wanda ya samu sabani da ubangidansa watau Nyesom Wike yana fuskantar barazana watanni da shiga ofis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laifin Nyesom Wike ko Siminialayi Fubara?
Anabs Sara-Igbe ya ce Nyesom Wike bai saurari umarnin da shugaban kasa Bola Tinubu ya bada na tsagaita wuta kan rikicin siyasar ba.
‘Dan siyasar ya ce Mai girma Simi Fubara ya yi bakin kokari na tabbatar da zaman lafiya, amma Ministan harkokin na Abuja bai hakura ba.
"Sauya-shekar wadannan ‘yan majalisa 27 zuwa APC yunkuri ne domin tabbatar da an cigaba da shirye-shiryen tsige (Gwamna).
Amma ya kamata su fahimci cewa su ‘yan jihar ne, amma jihar ta fi damuwa da halin da ake ciki a Ribas, ba mu son wata rigima."
- Anabs Sara-Igbe
Nyesom Wike ya bar PDP zuwa APC?
Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Nyesom Wike yana nan a PDP, shi bai koma APC ba.
Wani ‘dan majalisar dokoki a jihar Ribas, George Alabo, ya shaidawa duniya cewa har gobe Nyeson Wike bai sauya-sheka daga PDP ba.
Hon. George Alabo ya ce an samu baraka a PDP, saboda ganin shugabanni jam’iyyar sun gagara shawo kan lamarin, sai su ka shiga APC.
‘Dan majalisar yana takamar cewa mutanen mazabarsu suna tare da su kuma ko za ayi zabe, za su yi nasara a karkashin jam'iyya mai-ci.
Takarar shugaban kasan 2027 a PDP
Ana da labari jagora a PDP, Bode George ya ce jam’iyyarsu za ta mutu murus muddin daga Arewa aka sake dauko ‘dan takara a 2027.
George ya ce mutumin Arewa ba zai zama ‘dan takaransu na zaben shugaban kasa mai zuwa ba, ya ce dole yankin ya hakura sai 2031.
Asali: Legit.ng