Akpabio Ya Bayyana Gwamnan PDP da Sanatoci 2 da Za Su Iya Dawowa APC

Akpabio Ya Bayyana Gwamnan PDP da Sanatoci 2 da Za Su Iya Dawowa APC

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa mai yiwuwa gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, zai koma jam’iyyar APC nan ba da jimawa ba
  • A wajen taron bikin zagayowar ranar haihuwarsa a ranar Juma’a, Akpabio ya ƙara da cewa Sanata Aminu Tambuwal da Natacha Akpoti Uduaghan na iya koma wa APC
  • Kalaman na Akpabio sun biyo bayan zargin da Atiku Abubakar ya yi na cewa jam'iyyar APC da Bola Tinubu na kokarin mayar da Najeriya ƙasar jam'iyya ɗaya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Godswill Akpabio, Shugaban Majalisar Dattawa, ya bayyana cikin raha cewa wasu sanatoci da Gwamnoni a jam’iyyar PDP na iya ficewa daga jam’iyyar su koma jam’iyyar APC.

Shugaban Majalisar Dattawan ya bayyana hakan ne a yayin jawabinsa a bikin zagayowar ranar haihuwarsa da aka shirya masa a filin wasa na Godswill Akpabio International Stadium, Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, a ranar Juma’a, 8 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Babban lauya ya bayyana matsayin kujerun yan majalisa 27 na PDP da suka koma APC

Akpabio ya fadi wadanda za su dawo APC
Akpabio ya yi magana kan masu shirin dawowa APC Hoto: SPNigeria, Umo Eno, Natacha Akpoti Usuaghan
Asali: Twitter

PDP, NNPP, da sauran jam'iyyu na shirin yaƙar APC

A cewar tsohon gwamnan Akwa Ibom, "nan ba da jimawa ba, dukkanmu za mu zama iyali ɗaya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su haɗa kai da jam’iyyarsa domin ceto Najeriya daga jam’iyyar APC.

Atiku ya yi nuni da cewa manufar jam’iyya mai mulki ita ce ta mayar da Najeriya a matsayin ƙasa mai jam'iyya ɗaya.

A ranar Alhamis, 7 ga watan Disamba ne aka bayyana cewa jam’iyyun siyasa shida da suka haɗa da jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), sun ƙulla wani ƙawance da jam’iyyar PDP domin kalubalantar jam’iyyar APC.

Su wanene za su koma jam'iyyar APC?

Sai dai da yake magana a ranar Juma’a, Akpabio cikin raha ya bayyana Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom da Sanata Aminu Tambuwal daga Sakkwato da kuma Sanata Natacha Akpoti-Uduaghan a matsayin ƴan jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 3 da suka faru gabanin yan Majalisa 27 su sauya sheka daga PDP zuwa APC

Shugaban Majalisar Dattawan ya ce:

"Ina hasashen Najeriya mai girma a ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu, GCFR, Shugaban kasa kuma Kwamandan Sojoji. Kuma ina so in gode wa dukkan jam'iyyun siyasar da ke nan domin zaɓen shugaban ƙasarmu."
"Ko gwamnan wannan jihar (Eno na Akwa Ibom) har yanzu bai koma APC ba, ko za a iya tunanin hakan? Ina gaya muku wani abu, amma yanzu yana zaune kusa da matar mataimakin shugaban ƙasan Najeriya sannan tana zaune kusa da matar shugaban ƙasa sannan yana kusa da gwamnan Cross Rivers wanda ɗan APC ne."
"Sannan Gwamna Tambuwal, yanzu Sanata Tambuwal, yana tsaye kusa da ni. Abin da hakan ke nufi nan ba da jimawa ba zamu zama iyali ɗaya."

Ku kalli bidiyon a nan ƙasa:

An Ba Tinubu Shawara Kan Rikicin Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa an shawarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan rikicin siyasar jihar Rivers.

Ƙungiyar Ijaw Nation Congress ta buƙaci shugaban ƙasar da ya ja kunnen ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike kan iza wutar rikicin da yake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng