Gwamnan APC a Arewacin Najeriya Na Shirin Ketare Wa Zuwa Jam’iyyar PDP? Gaskiya Ta Bayyana
- Yayin da ake jita-jitar komawar Gwamna Alia Hyacinth jam’iyyar PDP, gwamnan ya yi martani kan lamarin
- Jam’iyyar APC reshen jihar na zargin gwamnan da yin fatali da jam’iyyar inda ta ce ya karkata zuwa jam’iyyun adawa
- Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin sakataren yada labaransa, Tersoo Kula a yau Lahadi 10 ga watan Nuwamba a Makurdi da ke jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue – Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue ya yi martani kan jita-jitar komawarsa jam’iyyar PDP.
Hyacinth ya yi wannan martani ne bayan yada wa da ake yi cewa ya gama shirya ficewa daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Wane martani gwamnan ya yi?
Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin sakataren yada labaransa, Tersoo Kula a yau Lahadi 10 ga watan Nuwamba a Makurdi da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar APC reshen jihar Benue ta na zargin gwamnan da watsi da lamuran jam’iyyar da kuma alaka da jam’iyyun adawa, cewar Daily Trust.
Alia ya ce wannan labarin kanzon kurege ne inda ya ce ya na aiki tukuru a kullum don ganin ya saka ‘yan jam’iyyar alfahari.
Sanarwar ta ce:
“Wannan ya nuna tsantsar yadda masu yada jita-jita su ka matsu da sharri, su na ci gaba da yada labaran karya madadin binciken gaskiya.
“Musamman karairayin da ake yada wa cewa an ana bai wa kwamitin Janar Lawrence Onoja mai ritaya da Emmanuel Jime kudade don yada jita-jita ga fadar shugaban kasa.
Wasu zarge-zarge gwamnan ya yi?
Gwamnan har ila yau, ya ce kwamitin ya na bata sunan Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume a kokarin cimma burinsa.
Alia ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin tabbatar da cika alkawuran da ta dauka wa mutanen jihar Benue, cewar PM News.
Sanarwar ta kara da cewa tun da jam’iyyar ba ta zargin gwamnan da rashin ayyukan alkairi ba ko kuma rashin jin dadin gwamnati a wurin al’umma, hakan ya nuna ana kan hanya.
Majalisa ta bukaci hana kananan hukumomi kudade
A wani labarin, Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta bar tura kudaden kananan hukumomi har sai an yi zabe.
Sanata Abba Moro shi ya bayyana haka a yayin zaman Majalisar inda ya ce hakan zai hana kama karya.
Asali: Legit.ng