Bayan Shan Kashi a Zaben Gwamnan Kogi, Dino Melaye Ya Bayyana Babban Darasin da Ya Koya

Bayan Shan Kashi a Zaben Gwamnan Kogi, Dino Melaye Ya Bayyana Babban Darasin da Ya Koya

  • Sanata Dino Melaye ya ce shiyyar sa ta Kogi ta Yamma ta tafka kura-kurai a zaɓen gwamnan Kogi da aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba
  • Ɗan takarar na PDP ya zargi sauran ‘yan takarar gwamna da suka fito daga Kogi ta Yamma da kin janye wa saboda shi
  • Tsohon sanatan ya ƙara da cewa zaɓen ya kuma nuna cewa Kogi ta Gabas ba zai iya samar da gwamna ba sai da goyon bayan wasu shiyyoyin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan Kogi, Sanata Dino Melaye ya bayyana darasin da ya koya a zaɓen ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.

Melaye ya zargi Leke Abejide na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da Olayinka Braimoh na jam’iyyar Action Alliance (AA) wadanda suka fito daga shiyyar sa ta Kogi ta Yamma da ƙin janye takararsu.

Kara karanta wannan

Kogi: SDP ta fadi dalili 1 da ya sa ta ki kalubalantar nasarar Ahmed Ododo

Dino Melaye ya magantu kan zaben Kogi
Dino Melaye ya bayyana kuskuren da ya yi a zaben Kogi Hoto: Dino Melaye
Asali: Facebook

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Melaye ya ce da Leke da Braimoh sun janye masa takara, da mutanen Kogi ta Gabas za su mara masa baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane kuskure yankin Dino Melaye ya yi?

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga jiga-jigan jam’iyyar PDP, mambobin ƙungiyar yaƙin neman zaɓensa da kuma magoya bayansa a wata liyafar cin abincin godiya a Abuja, ranar Juma’a, 8 ga watan Disamba.

A kalamansa:

"Idan da za a yi zaben da ya dace, ana mutunta tsarin dimokuradiyya, da ba haka abin yake ba. Idan akwai abin da ya kamata ku fahimta daga wannan zaɓen, to shi ne shiyyar Yamma ta tafka kuskure, ba gabaɗaya shiyyar Yamma ba, waɗannan dattijan. Wannan abun duba wa ne a wajen mafi yawan mu da muke nan."

Kara karanta wannan

Atiku da Ɗangote sun lale Naira biliyan uku sun baiwa ɗan takarar gwamna a arewa? Gaskiya ta yi halinta

“Gaskiyar magana ita ce, da sauran ƴan takara biyu daga shiyyar Yamma sun saurari muryar hikima a kan lokaci, da Leke da Braimoh sun janye a kan lokaci, irin ajandar da ta faru a Gabas ba za ta faru ba, saboda Gabas su ma sun ɓata, idon su ya rufe cewa Yamma ba ta da tsari."

Ya ƙara da cewa wani darasi shi ne an nuna wa mutanen Kogi ta gabas cewa ba za su iya samar da gwamna ba tare da goyon bayan wasu shiyyoyi ba.

"Wannan zaɓen kuma ya koyar da darussa da dama. Ɗaya daga cikin darasin shi ne cewa Gabas yanzu sun fi kowa sanin cewa ba za su iya samar da gwamna su kaɗai ba. Dole ne ku haɗa kai da wasu shiyyoyin domin zama gwamna.”

Shehu Sani Ya Shawarci Dino Melaye

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya shawarci Dino Melaye kan kotun da ya kamata ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen gwamnan Kogi.

Ya bayyana cewa idan Melaye ya yanke hukuncin zuwa kotu, to tabbas ta kasance kotun ta Tennis ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng